Hukumar EFCC ta fallasa waɗansu jami’an Ma’aikatar Shari’a su biyu, waɗanda su ka karɓi cin hanci, su ka cusa sunan Francis Atuche a jerin sunayen waɗanda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa afuwa.
PREMIUM TIMES ta ga wani rahoto a ranar Laraba, da EFCC ta aika wa sakatariyar Kwamitin Shawara Ga Shugaban Ƙasa Kan Yi Wa Ɗaurarru Afuwa (PACPM).
Waɗanda EFCC ɗin ta kama da laifi su ne shugaban sakatariyar ɗungurugum mai suna Emmanual Fan da wani mai suna Lawrence Marinus, wanda kafin hakan mamba ne na sakatariyar.
Dukkan su biyun dai an ɗauko su ne daga Ma’aikatar Harkokin Shari’a ta Tarayya, domin su yi aiki a sakatariyar kwamitin shawarar yin afuwar.
Rahoton na EFCC ya nuna akwai wanda ake zargi na uku, wanda shi ne ya biya kuɗin cuwa-cuwar. EFCC ta ce har yanzu ta na biye da shi, ta na so ta ƙure masa gudu.
Wannan kwamiti dai ya ƙunshi mutum 12, wanda Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami ne Shugaban Kwamitin. Ya aika wa Shugaba Muhammadu Buhari jerin sunayen mutum ya aika wa Buhari sunayen mutum 162 domin a yi masu afuwa. Ya aika da sunayen a ranar 14 Ga Afrilu, 2022.
An dai yafe wa mutum 159, aka yi fatali da sunayen mutum uku.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka ƙi yi wa afuwar har da tsohon Shugaban Bank PHB, Francis Atuche, wanda a cikin watan Yuni, 2021 aka ɗaure shi shekaru shida, saboda ya saci naira biliyan 27 daga bankin.
An gano an ƙaƙaba sunan sa ne tare da bayar da dalilin cewa “an yi masa afuwa saboda dalilin wata rashin lafiyar da ke neman kashe shi.” Amma sai kwamitin ya ƙi amincewa da hakan.
Amma a cikin watan Yuni, Malami ya aika wa EFCC takardar koken cewa wasu ne su ka ƙaƙaba sunan Atuche a jerin sunayen waɗanda aka nemi yi wa afuwar. Kuma takardar ƙorafin ta nuna cewa a cikin sakatariyar aka samu wasu ɓatagari su ka cusa sunan Atuche a jerin sunayen.
Daga nan fa sai EFCC su ka fara bin wasu mambobin kwamitin afuwa da ma’aikatan sakatariyar su na yi masu tsintar-farin-balbela ana yi masu tambayoyi.
An kuma yi gaba da waɗansu daga cikin mambobin ACJRD.
Yadda Aka Bayar Da Cin Hancin:
Yayin da wani rahoton EFCC ya tabbatar waɗanda aka kama da laifin su biyu sun karɓi maƙudan kuɗaɗen cin hanci daga hannun mutum na uku da EFCC ke neman kamawa har yanzu, wannan jarida ba ta kai ga gano ko nawa aka karɓa cin hanci don a maƙala sunan Atuche cikin waɗanda za a yi wa afuwar ba.
“Bincike ya nuna cewa Emmanual Ishaku Fan ya haɗa baki da Lawrence Marinus suka maƙala sunan Francis Atuche a rahoton sunayen da za a yi wa afuwa.
“Bincike ya nuna Emmanual Ishaku Fan ne ys karɓi kuɗaɗe a hannun ejan ɗin Atuche, daga nan ya yagi kason sa, ya damƙa wa Lawrence Minus na sa kason.” Inji rahoton EFCC.
Emmanual Fan ya musanta zargin da EFCC ke yi masa, yayin da ya ke amsa tambayoyin wakilin mu.
Shi kuma Lawrence Minus wakilin mu ya kasa samun sa, ballantana a ji ta bakin sa.
Discussion about this post