Idan aka yi la’akari da irin manyan hare-hare biyu da Boko Haram ɓangaren ISWAP su ka kai kwanan nan, alamomi na nuna mutanen fa tafe su ke kan hanyar su ta cika muradin da su ka bayyana na yin garkuwa da Shugaban Ƙasa.
A ƙarshen watan Maris na wannan shekara wani gungun su ya tare jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja za shi Kaduna, inda su ka kashe mutane kuma su ka yi gaba da mutum 62. Sun saki mutum 35 bayan sun karɓi kusan naira miliyan 100 daga kowanen mutum ɗaya da su ka saki ɗin.
Bayan gwamnati ta yi babbotai da cika-bakin za ta ceto su, daga baya ta yi watsi da waɗanda aka yi garkuwar da su, kowa ta sa ta fisshe shi. Aka har kowanen su ya na gaganiya da fafutikar biyan kuɗin diyyar fansar kai.
Katsam cikin Yuli kuma sai ISWAP ɗin dai su ka tura wani gungun mahara, tare da haɗin kan ‘yan Ansaru, shi ma wani ɓallallen yanki na Boko Haram wanda joni ne da Alƙa’ida, su ka yi wa Kurkukun Abuja da ke Kuje dirar-mikiya cikin dare. A take su ka kuɓutar da mutum 876, cikin su har da kwamandoji kuma gogarma-gogarman Boko Haram 64. Sai da su ka shafe awa uku su na duk abin da su ka ga dama a kurkukun.
Yayin da hankulan ‘yan Najeriya ya dugunzuma da farmakin Kurkukun Kuje, shi kuma Shugaba Buhari da duniyar da ke kewaye da shi, tsit ka ke ji, babu abin da ya yi, tamkar babu abin da ya faru.
Wani marubuci mai mai suna Ayn Rand ya ce, “Za ka iya kauda kai daga gaskiya muraran, amma ba za ka iya kaida kai daga abin da zai afka maka bakatayan idan ka ƙi tantagaryar gaskiya ba.”
Washegarin kai wa Kurkukun Kuje hari, Buhari ya kai ziyara, ya ga irin munin ɓarnar da aka yi, ya yi kakkausan tambayoyi, kuma ya yi alƙawarin ɗaukar mataki.
Ba a daɗe ba kuma sai su ka yi wa tawagar hadiman Buhari kwanton-ɓauna a cikin jihar sa ta haihuwa, Katsina. Bayan nan kuma su ka yi artabu da Bataliyar Gadin Shugaban Ƙasa, waɗanda su ne zaratan a-yi-ta-ta-ƙare da ake tutiya da su a ƙasar nan. Su ka yi gumurzu da su har suka kashe soja takwas a Bwari, kusa da Abuja.
Abu sai gaba-gaba ya ke yi. Sai su ka saki wani bidiyon da aka nuno su na dukan fasinjojin jirgin ƙasan da ke hannun su. Kuma su ka yi barazanar sayar da su. Ba su tsaya a nan ba, sun kuma yi alwashin kamo shuugabanni da sanatoci. “Da yardar Allah sai mun kamo El-Rufai da Buhari.”
Wannan barazanar kama shugaban ƙasa da sayar da kamammu tamkar yadda ake sayar da bayi, ta zo ne shekaru bakwai bayan kama ɗaliban Chibok su 276 a Jihar Barno.
Yanzu dai irin abin da Boko Haram su ka riƙa yi lokacin mulkin Jonathan har jam’iyyar su Buhari su ka samu damar kifar da gwamnatin sa, shi ne ISWAP ke yi a zamanin mulkin Buhari ɗin da kan sa.
Shekara takwas bayan kama ɗaliban Chibok, yanzu a zamanin mulkin Buhari an kama aƙalla yara 1,500 an yi garkuwa da su.
Garkuwa ta zama wata ƙwaƙƙwarar mummunar sana’a a ƙarƙashin gwamnatin Buhari, mutumin da aka riƙa zugugutawa cewa ai Janar ne na soja, wanda idan ya zama shugaba zai yi maganin sheɗanu da sheɗanci.
Ya zama abu mai muhimmanci Shugaba Buhari ya tashi ya sake yin bita da tilawar irin riƙon da ya yi wa Najeriya bayan ya yi alƙawarin bunƙasa ta fiye da yadda ya karɓe ta a 2015. Idan da a ce gwamnatin sa ta cika alƙawarin da ta ɗauka kan tsaro, to da kuwa mahara ko ‘yan ta’adda ba su samu sukunin miƙe ƙafa har su na barazanar sai sun kama shi ba.
Discussion about this post