Ƙoƙarin da jiga-jigan PDP ke kwana su na tashi da shi domin sasanta Gwamna Nyesom Wike da Atiku Abubakar na neman zama aikin banza, yayin da Wike ya garzaya kotu, ya na neman a ƙwace takarar da Atiku ya yi nasara a ba shi.
Wike ya ce shi ne ɗan takarar da ya yi nasara, domin Atiku ya tara yawan ƙuri’u ne ta haramtacciyar hanyar da ba bisa ƙa’ida ba.
A cikin kwafen ƙarar da Wike da wani ɗan PDP mai suna Newgent Ekamon su ka shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Wike ya nemi kotu ta ayyana shi matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP na zaɓen 2023.
Waɗanda Wike ya maka kotu sun haɗa da PDP, INEC, Atiku da Tambuwal. Kwafen takardun ƙarar sun nuna PDP ce ɗaya, shi kuma Atiku na biyu a jerin sunayen waɗanda ake ƙara.
A kwafen ƙarar mai lamba FHC/ABJ/C8/782/2022, Wike da Ekamon sun nemi buƙatu masu yawa da su ke neman kotu ta biya masu.
Waiwaye: Idan ba a manta ba, daidai fara zaɓen fidda-gwani na PDP a ranakun 28 da 29 Ga Mayu, Tambuwal ya ayyana janyewar sa, kuma ya nemi dukkan magoya bayan sa su zaɓi Atiku Abubakar.
Hakan da Tambuwal ya yi, ta sa Atiku samun ƙuri’u masu yawan da ya kayar da sauran ‘yan takara 12, cikin su kuwa har da Wike, wanda ya zo na biyu.
Wannan abu da Tambuwal ya yi ya fusata Wike ƙwarai, har ya kira Tambuwal maci amana. Duba da cewa a takarar 2015 wadda Atiku ya kayar da Tambuwal, Wike ɗin ya goyi bayan Tambuwal ne, ba Atiku ba.
Daga cikin ƙuri’u 767 da aka tantance a zaɓen fidda gwanin PDP na 2022, Atiku ya tashi da 371, Wike ya zo na biyu da ƙuri’u 237, Saraki na uku da ƙuri’u 70. Sai na huɗu Gwamna Udom Emmanuel na Akwa Ibom mai ƙuri’u 37.
Bayan Kammala Zaɓen Fidda-gwanin PDP:
Kwana ɗaya bayan kammala zaɓen fidda-gwanin takarar shugaban ƙasa na PDP, Wike ya riƙa bobbotai ya na ƙorafin cewa su Tambuwal, PDP da wasu ‘yan kudu sun ci amanar sa.
Lamarin ya ƙara muni bayan Atiku ya ɗauki Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta matsayin mataimakin takarar sa.
Wike A Kotu: Ni Na Ci Zaɓen Fidda-gwani, A Ba Ni A Huta:
Daga cikin abin da ƙorafe-ƙorafen Wike a kotu su ka ƙunsa, yawanci duk a kan ƙuri’un da Tambuwal ya sa aka zuba wa Atiku ne, har ya yi nasara a kan sa.
1. Wike ne ya ci zaɓen fidda-gwani ba Atiku ba.
2. Tambuwal ya janye daga takarar bayan lokacin da ya kamata ya janye ya wuce.
3. PDP ta bai wa Tambuwal dama ya yi magana sau biyu, inda sau ɗaya ya kamata a ba shi kuma a lokacin ya kamata ya ce ya janye, ba lokacin da za a fara jefa ƙuri’a a sake ba shi wani lokaci ba.
4. PDP ta mara wa Atiku baya, an jibga masa ƙuri’un Tambuwal don ya kayar da Wike.
5. Da ba a jibga wa Atiku ƙuri’un magoya bayan Tambuwal ba, to Wike ne zai kayar da shi, sai dai Atikun ya zo na biyu kawai.
7. Shin ƙuri’un Tambuwal da aka jibga wa Atiku sun haramta ko kuwa halastattu ne?
8. Shin daga lokacin da Tambuwal ya ce ya janye, ko ya na da sauran wani halasci a sha’anin zaɓen fidda-gwanin?
9. Shin daga lokacin da Tambuwal ya janye, ya rasa dukkan ƙuri’un sa, ko ya na da ikon da zai ce masoyan sa su zaɓi ‘wane’?
10. Shin ƙuri’un Tambuwal da aka danƙara wa Atiku sun halasta ko kuwa haramtattu ne?
11. Shin PDP ta yi ba daidai ba da ta nuna goyon bayan wani ɗan takara ƙarara a lokacin zaɓe, ko kuwa daidai ta yi?
12. Wike ya roƙi kotu a soke ƙidayar da aka yi, a sake ƙidaya ƙuri’un da aka jefa a wurin zaɓen fidda-gwanin.
13. Wike na so kotu ta haramta karkatar da ƙuri’un Tambuwal da aka yi zuwa ga Atiku.
14. Wike na so kotu ta yi fatali da takarar Atiku, ta ayyana shi halastaccen ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023.
Zuwa lokacin rubuta labarin dai ba a kai ga damƙa shari’ar a hannun kowane Mai Shari’a ba tukunna.
Discussion about this post