Shugaban kwamitin dattawan jam’iyyar PDP, Walid Jibrin ya bayyana cewa lallai jam’iyyar PDP ba ta yi adalci ba wajen rabon mukaman siyasa a jam’iyyar.
Jibrin ya yi wannan karin hake ne a lokacin da yake amsa tambayoyi da talbijin din Channels ranar Lahadi.
” Ace shugaban jam’iyyar Ayu dan Arewa ne, yankin Arewa ta tsakiya, nima shugaban kwamitin dattawan jam’iyyar dan Arewa ne daga jihar Nasarawa sannan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mu kuma dan yankin Arewa ne.
Sannan kuma game da rashin jituwa tsakanin Atiku Abubakar da Gwamnan Ribas Nysome Wike, Jibrin ya ce kwamitin dattawa ya kafa kwamiti domin haka kuma da zarar kwamitin ya mika rahoton sa za mu baiwa jam’iyyar shawara bisa abinda muka gano, kuma gaskiya kumai dacin ta za mu zayyana shi.
Idan ba a manta ba tun bayan zaben fidda gwani da Atiku ya kada Nysome Wike rashin jituwa ya barke tsakanin su. Wike na ganin an yi masa taron dangi ne aka kada shi kuma tun bayan haka ya daura damara yaki da haka.
Ana ta yin kokarin sasanta su amma abin ya ci tura.
Jam’iyyu da dama ciki har da APC suna zawarcin Wike ya mara musu baya domin samun nasara a zaben dake tafe. Hakan ya sa wasu na ganin Wike dai ba zai yi PDP ba a zaben shugaban kasa.
Discussion about this post