Kakakin Yaɗa Labaran Rundunar Kamfen ɗin Atiku Abubakar na PDP a takarar shugabancin ƙasa na zaɓen 2023 mai zuwa, Dumi Melaye, ya ce ‘yan hauragiyar soshiyal midiya ne kawai ke ɓata lokacin su wajen tunanin Peter Obi na jam’iyyar LP zai iya yin nasara.
Dino wanda aka tattauna da shi a gidan talbijjn na Channels, ya ce kwata-kwata Obi ba shi da makamai, albarusai da zafin hannun iya kai farmakin da zai samu ƙuri’un da za su kai shi ga yin nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Ya ce a cin zaɓe ana buƙatar mutum irin Atiku Abubakar na PDP zai iya haɗa kan ‘yan Najeriya a dukkan ɓangarorin da su ke wuri ɗaya.
Dino ya ce haɗin kan jama’a ne ƙashin bayan tattalin arzikin ƙasa, kuma shi ne ginshiƙin dimokraɗiyya.
Da ya ke buga misali, ya ce an sha samun irin su Peter Obi masu yi wa siyasa kumfar gishin-Andurus, amma idan zaɓe ya zo, ba su samun komai.
Dino ya buga misali da marigayi Gani Fawehinmi, wanda ya ce ya shiga takara cikin 2003, aka riƙa maganganu kan sa. “Amma duk da sunan da ya yi a kafafen yaɗa labarai, ƙuri’u 1,400 kacal ya samu a faɗin ƙasar nan.”
Melaye ya sake kafa hujja a Tunde Bakare, wanda ya ce an san shi, amma a wurin zaɓe bai taɓuka komai ba.
“Shi cin zaɓe ba surutai a Tiwita ko Instagram ba ne. Kuma Peter Obi da ake ta zugugutawa a soshiyal midiya, to ka shiga Tiwita ɗin da Instagram, za ka ga ba wasu mabiya shafukan sa ya ke da su masu ɗimbin yawa ba.” Inji Dino.
Da ya koma kan Tinubu, Dino ya ce ai tuni gwamantin Buhari ta goga wa takarar Tinubu kashin-kaji da baƙin fenti, saboda gazawar da gwamnatin ta yi.
A cewar sa, “gazawar da gwamnatin Buhari ta yi, ya zama wani kamfen ne ta yi wa Atiku da PDP. Domin Atiku a yanzu ya na da tabbacin lashe zaɓe sosai fiye da sauran ‘yan takara.” Inji Melaye.
Discussion about this post