Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa idan ba a canja fasalin Najeriya ba, to a haka ƙasar za ta ci gaba da tafiya cikin duhun matsalolin da su ka yi mata tarnaƙi da dabaibayi.
Ya bayyana haka ranar Alhamis Taron Shekara-shekara na 64, na Nazarin Littafin Linjila, wanda Majalisar Matasan Cocin Angalika su ka shirya a Ekiti.
Atiku wanda ɗan takarar sa na mataimakin shugaban ƙasa, Gwamnan Delta Ifeanyi Okowa ya wakilta, ya ce Najeriya na matuƙar buƙatar ƙwararru, masana kuma gwanayen shugabannin da za su karya lagon rashin shugabanci nagari, ta yadda za su ciyar da ƙasar nan gaba.
Ya ce abin da kawai ake buƙata a gwamnati mai ginannar alƙibla da tsarin federaliyya, shi ne bai wa kowane yanki na ƙasa ƙarfin iko da ikon mallakar albarkatun ƙasa sai kuma tabbatar da adalci, raba-daidai-gwargwado da kuma jawo kowane yanki a cikin gwamnati.
Atiku ya ce ya kamata Najeriya ta ci gaba da kasancewar ta federaliyya, amma fa ba a irin tsarin da ake tafiya a yanzu ba.
“Kowa ya sani a yanzu haɗin kai na fuskantar babbar barazana a Najeriya. Zargi da rashin gaskata juna a tsakanin ƙabilu daban-daban sai ci gaba da ruruwa ya ke yi, har ya kai munin da bai taɓa kaiwa a baya ba. Hakan na ƙara rura wutar masu so su ɓalle daga ƙasar nan.
“Kamar yadda na sha faɗa a baya, muddin za a riƙa damƙa harkokin tsaro ga wasu ɓangaren ƙabila ko mabiya addini ɗaya, to ba abin alheri ba ne ga haɗin kan ƙasar mu da kuma ci gaban ta.
“Najeriya za ta iya ci gaba idan aka kawar da ƙabilanci, bambancin addini da bambancin ƙabilanci, aka bijiro da haɗin kai tsakanin juna.” Inji Atiku.
Atiku ya yi alƙawarin idan aka zaɓe shi, zai kawo ƙarshen yajin aiki a jami’o’i, domin shi dama mutum ne mai bai wa ilmi muhimmancin gaske.
Ya ce babu ƙasar da za ta iya ci gaba alhali yara manyan goben ta na gida su na zaune ba su karatu an rufe jami’o’in su.
Discussion about this post