Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a APC, Kashim Shettima ya maida martani kan barkwancin da ake yi masa, dangane da shigar ‘gidadawan’ da ake cewa ya yi a wurin Taron Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya na 64 Legas.
Shettima dai ya yi je taron sanye da takalmin motsa jiki, irin shigar ‘yan tashe. Sannan kuma ya sanya kayan zamani (suit) wadda ta yi masa yawa. Sannan kuma ya ɗaura nektaye ka wanda bai tura shi cikin farar shet ɗin da ke ƙasan ‘suit’ ɗin sa ba.
An riƙa yaɗa hotunan shi zaune dirshasha kamar sabon shiga taro, kuma ana yi masa ba’a, shegantaka da kuma barkwanci.
Ganin yadda lamarin ya yi yawa sosai, Shettima ya fito ya yi bayanin cewa, “da gangan na yi shigar domin na cinkisa dandazon mutanen da aka ce min ba mu su ke goyon baya ba.
“Tun kafin na yi shirin fita na tura mutane na a wurin, sai mu ka ce min yawancin mahalarta taron za su yi ƙoƙarin cinkisar da ni.
“To dama ai na san taro ne na lauyoyi, kuma ni horon gogaggen ma’aikatacin bankin nan ne Jim Obia.”
Shettima ya ce ya gano cewa wani ɗan takarar shugaban ƙasa ne ya ɗauki nauyin yi masa barkwanci, amma dai bai faɗi sunan sa ba.
Daga ya ce kuma abin alfahari ne a gare shi da Tinubu cewa an yi taron a Victoria Island, tsibirin da yanzu ya koma ƙanƙareren birni albarkacin tsarin gyaran Legas da ɗan takarar APC Bola Tinubu ta fara ƙirƙirowa, lokacin ya na gwamnan Legas.
A wani labarin kuma, Shettima ya ce “idan aka zaɓe mu ni zan kula da tsaro, Tinubu zai kula da tattalin arziki.”
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na APC Kashim Shettima, ya bayyana cewa idan aka zaɓe su, shi zai fi maida hankali ne wajen tabbatar da samun tsaro.
Shettima wanda ya na cikin masu tattaunawa a Taron Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya a Legas, ya ce shi da kan sa zai jagoranci sojojin Najeriya wajen kakkaɓe ta’adda da ‘yan bindiga, yayin da Tinubu kuma zai maida hankali wajen inganta tattalin arzikin Najeriya.
“Na kasance cikin ruɗanin yaƙi tsawon shekaru 18, ni zan jagoranci sojoji, shi kuma oga na Tinubu zai maida hankali wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, tunda dama ‘hatsabibi ne wajen laƙanin tattalin arziki, duba da yadda ya maida Legas ƙasaitacciyar jihar da kusan ita ce ta uku a ƙasashen Afrika wajen ƙarfin tattalin arziki a lokacin sa.
“Idan Allah ya ba mu dama, ni zan kula da ɓangaren tsaro, zan jagoranci yaƙi a dukkan faɗin ƙasar nan.” Inji Shettima.
Sai dai kuma kalaman Shettima na nufin tamkar zai yi aikin da dokar ƙasa ta wajibta wa Shugaban Ƙasa ne, wato Babban Kwamandan Askarawan Najeriya.
Hakan ya sa an riƙa ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya idan ya na nufin zai ƙwace aikin shugaban ƙasa ne idan sun ci mulki, wato Tinubu.
Sashe na 130(2) na dokar 1999 ta ce Shugaban Ƙasa ne Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, shi ke da iko kan sojoji, ba mataimakin sa ba.
Babu wani sashe na dokar Najeriya da ta bai wa mataimakin shugaban ƙasa iko kan sojoji, ko da kuwa wata ‘yar ƙaramar bataliya ce.
Discussion about this post