Darektan kamfen ɗin ɗan takarar shugaban kasa na APC Bola Tinubu, kuma gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya aika da wasikar neman gafara bisa kalaman da yayi kan Paparoma.
A cikin wasikar, Lalong ya ce an lauya kalaman sa ne amma bai furta irin abubuwan da ake zargin ya ambata game da Paparoma ba.
A cikin wasikar sa na farko, Lalong ya karyata raɗeraɗin da ake ta yadawa wai Paparoma bai amince da mukamin shugaban Kamfen din Tinubu ba.
Ya ce ” Ni da kuke gani babban mabiyin cocin Katolika kuma cikakken domin har mukami ina da shi. Paparoma bai ce komai ba game da mukamin shugabancin darektan kamfen ɗin Tinubu ba.
” Wasu ne suke ta neman kago abinda bashi da karfin tsiya don su kawo ruɗani. A matsayina na jigo a jam’iyyar APC sannan shugaban kungiyar gwamnonin Arewa. Wannan siyasa ne ɗan da haka babu abinda ya hada addini da shi.
” Babu tilas a wannan harka, idan lokacin zaɓe yayi, kana da damar ka zaɓi wanda kake so, musulmine ko kirista, babu tilas. Amma adaina kawo ruɗani a cikin abin.
Lalon ya kara da cewa shi gwamna ne na kowa da kowa, musulmi ne kai ko kirista, kai ko ma wanda bashi da addini, doka ta ce kowa ya mulke shi da adalci.
” Wasu ne da suka runanin za a nadasu mataimakin shugaban kasa suke ruruta abin da ba haka ba. Suna kokarin sakala sunana a ciki kwamacalar su. Hanyar jirgi da ban na mota da ban.
A wasikar neman gafarar shugaban cocin Katolika, Lalong ya kara da cewa ba zai yi ko faɗi wani abu na cin fuska ko kawo kaskanci ga ɗarikar Katolika ko shugaban ɗarikar ba, wato Paparoma.
” Ni ɗinnan da kuke gani ina da muƙami a ɗarikar Katolika, saboda haka ba zan yi ko faɗi wani abu da zai kawo ƙasƙanci ga cocin ba. Amma bisa abubuwan da na faɗi, ina neman gafarar Paparoma da shugabannin cocin.
Discussion about this post