A kotun gargajiya dake Nyanya Abuja ne Maria Yakubu ta kai karan mijinta Gana Yakubu bisa zargin ya na saka tsafe-tsafe a gadin da take kwana akai don ya kashe ta.
Maria ta ce a dalilin haka ya sa take rokon kotu ta raba auren su da Yakubu.
“Tun da muka kammala gina gidan mu muka shiga Gana ya canja halin sa, bala’in yau daban na gobe. Kullum sai mun kaure da rikici.
“Wasu lokutan da gangar Gana yake dawowa gida da mace domin ya bani haushi amma sai in yo banza da shi.
“Wata rana bayan na dawo gida na ga an zuba garin magani akan gadon da nake barci. Dana tambayi Gana sai ya ce ba shi bane amma da ya shiga hannun ‘yan sanda sai ya ce shi ne ya aikata hakan.
“A dalilin haka ya sa nake so a raba auren mu saboda bana so na mutu a banza iyaye na su yi asara.
Alkalin kotun Shitta Abdullahi bayan ya saurari abin da Maria ta fadi ya daga shari’an zuwa ranar 8 ga Agusta.
Discussion about this post