Gwamnatin Tarayya ta bai wa kamfanonin jiragen sama wa’adin kwanaki 30 su biya biliyoyin kuɗaɗen da ta ke bin su bashi, ko kuma ta hana su ɗaukar fasinjoji a faɗin ƙasar nan.
Wannan barazana dai na nufin idan aka hana jiragen sama tashi, to dai dai kowa ya koma tafiya ƙasa a mota kenan. Ko kuma masu iyawa su yi fuka-fukai su riƙa tashi sama.
Gwamnatin Tarayya ta ce kuɗin da ta ke bin kamfanonin sufurin jiragen sama sun kai naira biliyan 19. Ba su ke nan ba. Ta ce kuma akwai wasu dala miliyan 7.6 su ma duk su na cikin kuɗaɗen da kamfanonin jiragen sama ɗin ba su biya ba, duk kuwa da cewa su na karɓar kuɗaɗe a hannun kwastomomin su.
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Ƙasa (NCAA) ce ta bayyana haka a ranar Talata.
NCAA ta ce maimakon su biya kuɗaɗen, sai kamfanonin jiragen sama su ka maida hankali bajen ɓata wa hukumar suna a kafafen yaɗa labarai. Haka dai Babban Daraktan NCCA, Musa Nuhu ya bayyana a Abuja, lokacin da ya ke ganawa da wakilan kamfanonin jiragen.
Nuhu ya ce kuɗaɗen hukumar waɗanda kamfanonin jiragen su ka riƙa sun haifar wa hukumar rashin jituwa da gwamnatin tarayya, domin kuɗaɗen shiga ne waɗanda NCAA ya kamata a ce ta damƙa su ga Gwamnatin Tarayya.
Ya ce haƙiƙanin gaskiya Gwamnatin Tarayya na matuƙar buƙatar kuɗaɗen a yanzu da ta ke cikin matsanancin halin rashin kuɗaɗe.
Kungiyar Kamfanonin Jiragen Cikin Gida (AON) a na su ɓangaren, sun zargi NCAA da laifin ɗirka masu haraji na babu gaira babu dalili daban-daban.
Cikin wata wasiƙa da su ka aika wa Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed, sun ce yawan haraji daban-daban da aka ɗirka masu a daidai lokacin da dala ta yi tsada, man da jirage ke amfani da shi ya yi tsada shi ma kuma ya na wahala, to abin ya yi masu yawa da kuma tsanani sosai.
Nuhu ya ce “zargin da kamfanonin ke yi duk na rashin adalci ne kuma maras dalili da kuma ƙoƙarin shafa wa hukumar NCAA baƙin fenti.”
Ya ce dukkan kamfanonin jiragen saman ƙasar nan sun riƙe bashin NCAA, na Hukumar Tashoshin Jiragen Sama (FAAN) da kuma na Hukumar Kula da Sararin Saman Najeriya (NAMA).
Nuhu ya ce rabon da NCAA ta yi ƙarin haraji ga kamfanonin jiragen sama tun shekaru 13 da su ka gabata.
Discussion about this post