Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa ta fahimci wasu matsalolin tsaron da su ka addabi ƙasar nan, daga wasu ƙasashe ne aka yi sumogal ɗin shigo da su Najeriya.
Shugaba Buhari ya furta haka a wurin bukin yaye ɗalibai na 30 na Kwalejin Tsaro ta Ƙasa, ranar Juma’a, a Abuja.
Buhari wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya wakilta, ya ce Najeriya da Afrika na fuskantar matsanancin yanayi na fama da ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da sauran tantiran ɓatagarin da su ka hana yankuna daban-daban zaman lafiya.
Ya ƙara da cewa tuni dai gwamnati ta bayar da umarni ga sojoji da sauran jami’an tsaro su gaggauta kakkaɓe waɗannan masu hana jama’a zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya ce sojoji sun yi nasarar kakkaɓe ‘yan Boko Haram, waɗanda su ka hana yankin Arewa maso Gabas zaman lafiya. Ya ce a yanzu an takura su, babu mafita sai saranda su ke ta yi, kuma dubban su jami’an tsaro na kula da su.
“Gwamnati ta damu sosai da matsalar ‘yan bindiga da sauran ɓatagari, waɗanda su ke ƙwan su su ƙyanƙyashe shi a nan cikin sassan ƙasar nan.
“Saboda idan aka duba, za a ga cewa yawan hare-haren da ake kai wa jama’a sai ƙaruwa su ke yi. To ba za mu lamunci wannan ba.
“Kuma mun bai wa dukkan jami’an tsaro kakkausan umarnin kakkaɓe ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da dukkan sauran masu tayar wa ƙasar nan ƙayar baya.
“Ina so na tabbatar wa dukkan ‘yan Najeriya cewa gwamnati na dukkan ƙoƙarin ganin ta murƙushe ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da sauran ɓatagari, kuma a kama na kamawa, a hukunta su, a duk inda su ke a ɓoye.”
Buhari ya jinjina wa Kwalejin Tsaro ta Ƙasa saboda shaharar da ta yi wajen yaye ƙwararrun jami’an sojoji waɗanda kan zama shugabannin ɓangarorin tsaron ƙasa da da sauran su.
Discussion about this post