Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa a duk shekara ana samun asarar naira tiriliyan 3.5 a harkokin noma, bayan an kammala girbin amfanin gona.
Ƙaramin Ministan Noma da Bunƙasa Karkara, Mustapha Shehuri ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi wurin taron miƙa wa Cibiyar Binciken Kayayyakin Da Suka Daɗe Ajiye satifiket na ingancin aiki, wato (ISO) na Ƙasa-da-ƙasa, a Abuja.
Shehuri wanda Daraktan Ƙasa da Kula da Canjin Yanayi, Shehu Bello ya wakilta, ya ce irin asarar da ake ɗibgawa bayan kallama girbin amfanin gona a ƙasar nan, ta na haifar da wawakeken giɓi wajen samun bunƙasar tattalin arzikin cikin gida (GDP).
“Asarar da ake ɗibgawa bayan kammala girbin amfani gona a ƙasar na ta yi yawan da ta ke kawo babbar barazana wajen wadatar abinci a Najeriya.
“Kusan kashi 50 zuwa 60 bisa 100 na kayan marmari a ƙasar nan, ba a killace su yadda ya kamata, ta hanyar da za a daɗe ana cin mariyar su. Abin takaici har yau an ƙi maida hankali wajen yadda za a daɗe ana samun kuɗi da su. Sai dai kawai a fi maida hankali wajen noman su kaɗai.
“Ƙungiyar Action Aid ta ba mu rahoton cewa aƙalla ana yin asarar naira tiriliyan 3.5 a duk shekara bayan kammala girbin kayan gona. Hakan kuwa na haifar da wawakeken giɓi sosai ga inganta tattalin arzikin cikin gida a fannin noma (GDP).
“Amma wannan Cibiyar Binciken Kayan Gona ta yi shirin shawo kan waɗannan matsaloli ta hanyar samar da wadatattu kuma ingantattun kayan aiki ga jami’an bincike.”
Shehuri ya yaba da ingancin ɗakin gwajin cibiyar, wanda ya ce samar da shi ya nuna cewa lallai cibiyar da gaske ta ke yi wajen buri da ƙudirin da ta ɗauka. Musamman ganin cewa babu irin dakin gwajin a duk sauran ƙasashe yankin Saharar Afirka.
Sai dai kuma ya hore su da ci gaba da kasancewa su na aiki mai inganci, inda ya ƙara da cewa satifiket ɗin da aka ba su, ba na dindindin ba ne har abada. Ya ce da zaran sun yi aiki jigari-jigari, to za a soke katin shaidar ingancin aikin da aka ba su.
Discussion about this post