An ƙulla yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Tarayya da wasu kamfanoni biyu na Isra’ila da Japan, domin su ƙera wa Najeriya babura waɗanda ba su amfani da fetur.
Baburan za su sauƙaƙe wahalhalun amfani da fetur, rage gurɓacewar yanayin da hayaƙi ke yi da sauƙin sarrafawa a harkokin sufurin marasa ƙarfi.
Ƙasashen Isra’ila da Japan za su ƙera wa Najeriya babura masu aiki da wutar lantarki
An ƙulla yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Tarayya da wasu kamfanoni biyu na Isra’ila da Japan, domin su ƙera wa Najeriya babura waɗanda ba su amfani da fetur.
Baburan za su sauƙaƙe wahalhalun amfani da fetur, rage gurɓacewar yanayin da hayaƙi ke yi da sauƙin sarrafawa a harkokin sufurin marasa ƙarfi.
An ƙulla yarjejeniyar ce tsakanin Najeriya wadda Hukumar NASENI ta wakilta da kuma kamfanonin biyu a Abuja, a ranar Alhamis.
Jakadan Isra’ila a Najeriya Micheal Freeman ya ce wannan aikin ƙerawa da haɗa baburan, haɗin gwiwa ne tsakanin kamfanonin Isra’ila da Japan, domin sauƙaƙe wa dimbin jama’a hanyoyin zirga-zirga.
Mataimakin Shugaban Hukumar NASENI Mohammed Haruna ya bayyana cewa wannan gagarimin aiki zai hanzarta fara ƙera ababen hawa a Najeriya, kamar yadda shi ma Shugaban Kamfanin Fito Wadada Aliyu ya ƙara tabbatarwa.
Shugaban kamfanin SIXAI mai suna Sasi Shilo, ya ce Japan na nan kan ƙoƙarin ta na samar da sauƙin rayuka ba ga ‘yan Najeriya kaɗai ba, har ma ga sauran ƙasashen Afrika baki ɗaya.
An ƙulla yarjejeniyar ce tsakanin Najeriya wadda Hukumar NASENI ta wakilta da kuma kamfanonin biyu a Abuja, a ranar Alhamis.
Discussion about this post