Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya biya tallafin karatu EUR 232,000 ga dalibai ‘yan asalin jihar Zamfara dake Karatu a kasar cyprus.
Kwamishinan yada labarai Ibrahim Dosara ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Gusau a farkon wannan Mako.
Dosara ya ce babban bankin Najeriya CBN zai biya kudaden kai tsaye zuwa asusun ajiyar kowani ɗalibi dake karatu a kasar.
Ya ce kudin na daga cikin EUR 297,509.11 da ya kamata gwamnati ta biya daga shekarar 2021 zuwa 2022 wanda ya hada da kudin abinci, wurin zama da kudin makaranta.
” Daga cikin kudin gwamnati za ta biya EUR 23,157.00 kudin izinin zama a kasar sannan EUR 8,843.00 a biya wa daliban.
“Gwamnati ta yi kira ga dalibai, iyayen daliban da jami’ar da daliban ke karatu da su kara hakuri da gwamnati cewa nan ba da dadewa ba daliban za su ci gaba da karatunsu.
“Gwamnati ta yi kira ga gidajen jaridu su rika tabbatar da sahihancin labarai kafin su yada domin labaran da aka rika yadawa wai gwamnati bata kula da dalibai ba gaskiya bane.
Dosara ya ce gwamnati ta dauki nauyin karatun dalibai su yi karatun darussan kimiyya a jami’o’in kasashen Cyprus, US, UK, Netherlands, India da Sudan.
Discussion about this post