Babban Bankin Najeriya CBN ya umarci bankunan Najeriya su ƙara wa masu ajiya a ƙarƙashin tsarin ‘savings’ kuɗin ladar ajiya daga kashi 0.15 zuwa kashi 4.2 bisa 100.
Wannan umarnin ƙarin kuɗi kuma a cewar CBN ya fa ne daga ranar 1 Ga Agusta, 2022.
Cikin wata sanarwa da CBN ya fitar a ranar 15 Ga Agusta, 2022, wadda Daraktan Sashen Sa-ido Kan Harkokin Bankuna ya sa wa hannu, an ce an maida kuɗin ruwan daga kashi 10 zuwa kashi 30 bisa Tsarin Hada-hadar Kuɗaɗe na MPR.
Cikin watan Yuli ne CBN ya ce ya ƙara kuɗin ruwan daga kashi 13 zuwa kashi 14 bisa 100. Kuma wannan ne karo na biyu da CBN ya yi ƙarin kuɗin ruwan a cikin 2022.
“Idan za a iya tunawa, a ƙoƙarin da CBN ya yi domin rage raɗaɗin ƙuncin korona, CBN ya rage mafi ƙarancin kuɗin ruwa na kuɗaɗen ajiya daga kashi 30% zuwa 10%, domin a ƙara wa tattalin arzikin ƙasa karsashi.” Inji CBN.
“Bayan wucewar korona kuma, ganin yadda yadda tattalin arziki ke wutsilniya, hakan ya sa CBN ke ganin ya zama wajibi a sake saisaita kuɗin ruwan ladar ajiya na kuɗaɗen naira, ba na Kuɗaɗen ƙasashen waje ba.”
“Saboda haka, daga ranar 1 Ga Agusta, 2022, mafi ƙanƙantar kuɗin ruwan ajiyar kuɗaɗen asusun ‘savings’ zai kasance daga kashi 30 bisa 100.”
Hakan dai na nufin kwanan nan masu ajiya a tsarin ‘fintech’ za su riƙa arcewa su na komawa tsarin ‘savings’, saboda garaɓasar da za’a riƙa samu daga bankuna.
Discussion about this post