Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala-Buni ya bayyana cewa gwamnatin jihar Yobe ta baiwa ƴaƴan marigayi Sheikh Goni biyu aiki a jihar Yobe.
Mala-Buni ya bayyana haka da ya ke ganawa da iyalan marigayin a fadar gwamnatin jihar ranar Talata.
Mala-Buni ya kara da cewa gwamnatin Yobe zata cigaba da kula da iyalan mamacin.
Yadda wasu sojoji suka kashe sheikh Goni daga taikamakon rage hanya
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Yobe ta tabbatar tare da bayyana yadda Lance Kofur John Gabriel ya kashe Sheikh Goni Aisami a Jihar Yobe.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Yobe, Dungus Abdulkarim ya fitar, ya ce Gabriel wanda yanzu haka yake hannun su shi da wani sojan da ya yi ƙoƙarin taya shi tserewa da motar malamin, dama can a wannan daren da abin ya faru, ya yi niyyar fita ya tare motoci ne domin ya yi fashi da makami.
“John Gabriel da Adamu Gideon duk su na aiki ne a Bataliya ta 241 da ke Nguru. Gabriel shi ne soja mai lamba NA/13/69/1522, shi kuma Gideon NA/13/70/6552.
“Gabriel ya fito daga barikin sojan Nguru ne da niyyar tafiya fashi da makami ta hanyar tare motocin matafiya. Ya fito ya tsaya a shingen sojoji ɗauke da ɗan gadon kambed, wanda ba a sani ba ashe ya naɗe bindiga ya ɓoye a cikin gadon.
“Ya tsaye sai ga Sheikh Goni Aisami Gashuwa, a mota ƙirar Honda mai lamba KBT 31 AE, inda Gabriel ya tsayar da shi, ya ce ya rage masa hanya.
“Su na tafiya an kai wajen Jaji-Maji cikin Ƙaramar Hukumar Karasuwa, sai soja Gabriel ya ce Malam ya tsaya, kamar ɗaya tayar gaba ta na ƙara.
“Ko da Malam ya fita domin ya duba taya, sai Gabriel ya ɗirka masa bindiga, sannan ya ja gawar sa, ya kai ta can cikin daji.”
Abdulkarim ya ƙara da cewa soja Gabriel ya kira abokin sa soja Adamu Gideon domin ya taimaka masa, bayan ya kasa guduwa da motar malamin, saboda ta ƙi tashi.
Ya ce wani mai wucewa zuwa gona ne ya ga gawar malamin a daji da kuma mota, ya garzaya ya sanar wa ‘yan sandan Jaji-Maji, waɗanda su ka duƙufa aikin su, har su ka kamo sojojin biyu.
Kakakin ya ce jami’an ‘yan sanda sun samu bindigar sojan da kuma wata mota ƙirar Sharon a wurin da aka yi kisan.
“Tuni dai wanda ya yi kisan ya amsa laifin sa.” Inji Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Jihar Yobe, Dungus Abdulkarim.
PREMIUM TIMES dama ta buga labarin cewa soja Gabriel tsohon ɓarawo ne, ya taɓa yi wa Kwamandan Bataliyar Sojojin 241 da ke Nguru satar naira 480,000, har kwamandan ya tsine masa, kuma ya ce da yardar Allah Gabriel ba zai yi kyakkyawan ƙarshe ba.
Discussion about this post