Majalisar Tarayya ta umarci Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed ta gaggauta bayyana domin gabatar da adadin kuɗaɗen da aka biya dalla-dalla, da sunan biyan talalfin fetur.
Shugaban Kwamitin Binciken Kuɗaɗen Fetur, Aliyu Musa ne ya bayar da wannan umarni a ranar Talata, lokacin da Daraktan Harkokin Kuɗaɗe na Cikin Gida a Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe ya bayyana a gaban kwamitin.
Kwamitin dai tun da farko ya bayar da wa’adin zuwa ranar 16 Ga Agusta domin a kai masa kwafen bayanan da su ka haɗa da:
Jimla da dalla-dallar adadin kuɗaɗen da aka gabza daga cikin Asusun Haɗaka na tara kuɗaɗen haraji aka biya tallafin fetur da su, tun daga 2013 zuwa yau 2022 da ake ciki.
Kwamiti ya kuma nemi a kai masa dukkan kwafe-kwafen takardun biyan kuɗaɗen da aka ce an yi.
Kwamitin bincike ya kuma nemi a kai masa sunayen dukkan kamfanonin da aka taɓa biya kuɗaɗen tallafin fetur da adadin da aka riƙa biyan kowane.
Wannan tashin-balli ya zo ne bayan Minista Zainab ta bayyana cewa Najeriya na buƙatar naira tiriliyan 6.7 domin ta biya tallafin fetur da kuɗaɗen.
Aliyu ya ce wannan lamari abin damuwa ne matuƙa.
“Dole Minista ta bayyana domin gabatar da bayanai masu damun ‘yan Najeriya. Ciki har da shirin da gwamnati ke yi domin ciwo bashi a biya tallafin fetur da kuɗaɗen bashin.
Wanan binkice na faruwa ne makonni biyu bayan Minista Zainab ta ce tattalin arzikin Najeriya ya kusa durƙushewa; an gano saura dala biliyan 15 a asusun waje, ba dala biliyan 36 da CBN ya ce saura ba.
Yayin da Najeriya ke shirin zaɓen 2023 cikin shekara mai zuwa, hujjoji na ƙara bayyana cewa tattalin arzikin ƙasar fuskantar matsanancin yanayi biyu: wato baitilmalin da ba ko ranyo a ciki, sai kuma raguwar da tattalin ke yi a kullum.
Jami’an gwamnati da manyan ‘yan kasuwar da ke da masaniyar halin da ake ciki, sun ce ana nuna damuwa sosai a Abuja da Legas, yayin da wani zaɓaɓɓen jami’in gwamnati ya jawo hankalin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele cewa abin da ya rage a asusun Najeriya da ke waje fa bai wuce dala biliyan 15 ba, wato ƙasa sosai da dala biliyan 36 ɗin CBN ɗin ya yi iƙirarin cewa su na cikin asusun.
Yayin da Najeriya ta kashe naira tiriliyan 5.9 wajen shigo da kayayyaki daga waje tsakanin Janairu zuwa Afrilu 2022 kaɗai, dala biliyan 15 kacal ɗin ƙasar ke da shi a yanzu ba su wuce kashewa cikin watanni huɗu kacal ba kenan wajen shigo da kayayyaki.
Masana harkokin tasarifin kuɗaɗen sun ce da a ce komai na tafiya daidai, to raguwar kuɗaɗen ba abin damuwa ba ne. Amma abin fargabar shi ne yadda aka shafe watanni shida cur Najeriya ba ta zuba ko sisi a cikin asusun don kuɗin su ƙaru ba. Wannan kuma ya faru ne saboda matsalar rashin wadatar ɗanyen man da Najeriya ke fitarwa waje ne, da kuma tsayuwar gwanin jakin da kasuwar ta yi.
Sannan kuma ɗaukar lokaci mai tsawo da NNPC ta yi ta kada zuba cinikin ɗanyen mai a CBN, shi ne ya haifar da tsawwala farashin dala a kasuwannin ‘yan canji.
Wata babbar ma’aikaciyar banki wadda ta ce wannan jarida ta rufa mata asiri kada ta ambaci sunan ta, ta ce an daɗe ana ɓoye gaskiyar sauran adadin kuɗaɗen gwamnati a cikin asusun waje, wanda babbar matsala ce sosai a halin yanzu.
Ta ce an yi ƙarin gishiri ne wajen ainihin yawan kuɗaɗen da ke CBN, domin kawai a ɓoye ainihin adadin da su ka rage a asusun waje.
An haƙƙaƙe cewa wannan babban jami’in gwamnati wanda kuma zaɓen sa aka yi, ya sanar wa Shugaba Muhammadu Buhari gaskiyar halin da ake ciki na ramewar tattalin arzikin Najeriya. Sai dai kuma Fadar Shugaban Ƙasa ba ta amsa wa PREMIUM TIMES tambayoyin da ta yi kan wannan mawuyacin halin da ake ciki ba.
Sannan kuma maida NNPC hannun jarin masu kasuwanci da aka ce an yi, ya ƙara dagula matsalolin. Wato tunda NNPC ya kasa zuba kuɗaɗen cinikin ɗanyen mai ko na fetur a asusun CBN, tilas kenan bankin ya tashi ya inda zai samu manyan kuɗaɗen ƙasashen waje.
Abin damuwa a nan shi ne, mafi yawan hanyoyin da CBN zai iya samun kuɗaɗen duk a toshe su ke da majinar murar da ta toshe hancin CBN ɗin, wanda kuma shi da kan sa ya ƙirƙiri tsarin da ya haifar da toshewar ƙofofin hancin na sa.
Ma’ana dai tunda asusun ajiyar kuɗaɗe na waje an kasa saka masa komai tsawon watanni huɗu, to ƙasar nan ba ta da sukunin iya biyan kuɗaɗen abinci, magunguna da kayan ayyuka daban-daban da ake buƙatar shigo da su a masana’antun mu. Wato dai irin matsalar tattalin arzikin da Sri Lanka ke fuskanta a yanzu kenan.
Maganar dai kai tsaye ita ce Najeriya na fuskantar mummunar matsalar ƙarancin kuɗi, ga wawakeken giɓin kasafin kuɗi, tulin basussuka da kuma taguwar da kuɗaɗen shigar da ƙasar ke samu ke yi a kullum.
Cikin Yuli PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda matsalar ƙarancin kuɗaɗe ta yi wa Najeriya rumfa inda a cikin watannin Janairu zuwa Afrilu kuɗaɗen da ƙasar ta biya bashi, sun haura kuɗaɗen shigar da ta samu a cikin waɗancan watannin huɗu.
Kafin NNPC ta kasa ci gaba da zuba kuɗin cinikin ɗanyen mai a CBN, a duk wata ta kan zuba dala biliyan 3 daga ɗanyen man da Najeriya ta sayar a watan. Amma kuma kusan shekara ɗaya kenan NNPC ba ta zuba abin da ya kai ko da dala miliyan 200 ba.
Cikin watan jiya ne Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya ce a kwantar da hankali tare da yin taka-tsantsan, saboda fatara da talauci sun yi wa Najeriya tarnaƙi da dabaibayi. Ta kai babu kuɗaɗen da ƙasar za ta biya manyan ayyukan raya ƙasa a shekara mai zuwa. Hakan na nufin lamarin zai ƙara munana matsalar rashin aikin yin da ake fama da ita, sai kuma ƙaruwar malejin ƙuncin rayuwa da hakan zai haifar kenan a shekara mai zuwa.
Cikin makon juya ne kuma Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed ta ce Gwamnatin Tarayya ta kamfaci dala biliyan 1 daga Asusun Rarar Kuɗin Fetur, domin inganta tsaro.
Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed, ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kwashi naira biliyan 1 daga Asusun Rarar Kuɗin Fetur (ECA), domin inganta harkokin tsaro, a daidai lokacin da kuɗaɗen shiga daga fetur ke ƙara raguwa sosai.
Zainab ta yi wannan bayani a gaban manema labarai, ranar Laraba, a fadar Shugaban Ƙasa, ƙarshen zaman su da Shugaba Muhammadu Buhari.
Waɗannan kuɗaɗe da Zainab ta ce an kamfata, lamarin ya zo ne daidai lokacin da ake kukan cewa kuɗaɗen asusun sun ragu sosai da sosai.
Rahotanni sun ce kuɗaɗen da ke cikin asusun sun ragu daga dala miliyan 35.7 a cikin Yuni 2022 zuwa dala 376,65.09 a ranar 25 Ga Yuli, 2022.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa Akanta Janar ne ya bayyana sauran adadin a ranar Talata, amma bai faɗi dalilin raguwar kuɗaɗen ba.
A ranar Laraba dai Minista Zainab ta ce wutsilniyar da kasuwar ɗanyen mai ke yi a duniya ce ta tankwafe asusun har kuɗaɗen su ka ragu.
“Tsawon shekaru huɗu kenan ba mu saka ko sisi a cikin Asusun Rarar Ribar Fetur ba, saboda faɗi-tashin da kasuwar ɗanyen mai ke yi a duniya.” Inji Zainab.
“To abin da mu ke da shi a cikin asusun ne mu ka riƙa cira a hankali ana yin wasu ayyuka da su. Kuma duk lokacin da za a yi amfani da kuɗaɗen, sai an nemi shawarar Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa, wato gwamnoni, saboda asusu ne na Gwamantin Tarayya.
“Kuɗin da aka cira daga asusun a baya-bayan nan, su ne dala biliyan 1 domin a inganta harkokin tsaro. Kuma duk abin da ake cira sai da sanin Gwamnoni.”
Discussion about this post