Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike, ya zargi tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamiɗo cewa shi da wasu ‘yan a ɓaras ne su ka haddasa wa PDP faɗuwa zaɓen 2015.
“Ba batun ba a ne ba, babu wanda ɗauki irin su Sule Lamiɗo da muhimmanci. Mutumin da ya na jigo a PDP amma jam’iyyar sa ta faɗi zaɓe sau biyu a jere a Jihar Jigawa.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Wike mai suna Kelvin Ebiri ya fitsr a ranar Laraba a Fatakwal, Wike ya maida wa Lamiɗo raddin caccakar da ya yi masa ce a gidan talbijin na Channels, inda ya ce Wike bauta ya ke so ‘yan Jihar Ribas su riƙa yi masa.
Ebiri ya bayyana Wike cikakken ginshiƙin PDP, kuma ya ce PDP ta yi nasara a Ribas cikin 2015 da 2019, amma kuma ta faɗi zaɓe a Jigawa cikin 2015 da 2019 a kan idon Lamiɗo.
Daga nan ya bayyana cewa kalaman da Lamiɗo ya yi kan Wike ba su dace ba, don kawai Lamiɗo ɗin ya na goyon bayan Atiku Abubakar.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da Sule Lamiɗo ya yi wa Wike wankin-babban-bargo saboda Atiku.
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamiɗo, ya ragargaji Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas a kan rigingimun da ke faruwa a cikin jam’iyyar.
A wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV ya yi da shi a ranar Talata, Lamiɗo ya ce nan da watanni takwas Wike zai zama mujiyar da kowa zai riƙa gudun sa bayan ya sauka daga muƙamin gwamna da ya ke tutiya da shi a yanzu.
Lamiɗo wanda makusancin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ne, ya ce shisshigi da wuce makaɗi da rawar da Wike ke yi, ba zai haifa masa ɗa mai ido bayan ya sauka daga mulki ba.
“Shi Wike ya na halayya ce irin ta mulkin Fir’aunanci, wadda sai idan ‘yan jihar sa sun maida kan su bayi ne kaɗai za su iya bin sa.”
Lamiɗo ya yi tir da irin kakkausan kalaman da ya ce Wike na fesawa idan ya na magana tamkar wani ɗan jagaliya.
Bayanan Lamiɗo sun zo daidai lokacin da ake ta ƙoƙarin ganin an sasanta Wike da Atiku, kuma kwana ɗaya bayan an ce Wike da makusantan sa sun gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu.
“Surutai da bobbatan da Wike ke yi, ana fa tsayawa a saurare shi ne don kawai ya na gwamna. Amma ba don wani wai shi Wike ne ke magana ba.
“Ka dubi abin da ya ke yi a jihar sa. Mutum 13 ya fito takarar fidda gwani na zaɓen gwamna. Amma Wike ya yi masu ƙarfa-ƙarfa, ya ɗora wanda ya ke so. Kuma dukkan sauran sun fusata da shi.
Da ya ke magana kan masu cewa a sauke Shugaban PDP, Iyorchia Ayu saboda ya fito daga Arewa, yankin da ɗan takarar shugaban ƙasa ya ke, sai Lamiɗo ya ce shi ba ya goyon bayan a sauke shi. “Saboda ai ba wannan ne karon farko da ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito yanki ɗaya da shugaban PDP na ƙasa ba.” Inji Lamiɗo.
“A zaɓen 2007 da marigayi ‘Yar’Adua ya yi takara, Ahmadu Ali ne shugaban PDP, daga Jihar Kogi. Saboda haka ai shugaban jam’iyya ba shugaban ƙasa ba ne. Ko kaɗan ba haɗa su. Sai mu ka ce a bari sai bayan an ci zaɓe sai a sauya.” Inji Lamiɗo.
Daga cikin rigimar da ake yi da Wike dai har da neman a cire Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayu, saboda ya fito daga Arewa, yanki ɗaya da Atiku da ke takarar shugaban ƙasa.
Discussion about this post