Gwamnonin Najeriya sun kai wa Shugaba Muhammadu Buhari shawarwarin da su ke ganin yin hakan zai sa Najeriya ta kauce daga durƙushewar tattalin arziki.
Cikin wata ziyara da su ka kai masa a Yuli, majiyar da ta san wainar da aka toya, ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa gwamnonin sun bayar da shawarwarin hanyoyin da Najeriya za ta rage kashe kuɗaɗe barkatai.
Daga cikin hanyoyin, shawara ta farko da gwamnonin su ka bayar ita ce a sallami duk wani ma’aikacin Gwamnatin Tarayya, wanda ya wuce shekara 50 a duniya kawai. A sallame shi tare da biyan sa kuɗin sallama, a wuce wurin.
Gwamnonin sun bijiro da waɗannan tsauraran shawarwari ganin yadda tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da fuskantar babbar barazana.
Aƙalla dai akwai ma’aikatan gwamnatin tarayya su 89,000, waɗanda a shekarar 2022 albashin su zai kai naira tiriliyan 4.1, daga cikin kasafin naira tiriliyan 17 da Najeriya ta yi.
To sai dai kuma ba a san ko waɗanda su ka haura shekaru 50 su nawa ba ne, kuma gwamnonin ba su faɗi nawa ake kashewa wajen biyan su albashin ba.
Gwamnonin sun kuma nemi Gwamnatin Tarayya ta gaggauta yin amfani da Rahoton Kwamitin Stephen Oronsaye. Wannan kwamiti dai tun cikin shekarun baya ya bayar da rahoton shawarar a kashe duk wata ma’aikata ko hukumar da aikin ta ya yi kama ko iri ɗaya da aikin wata ma’aikatar ko hukuma, domin a rage kashe kuɗaɗe.
Dangane da barazanar durƙushewar tattalin arziki kuwa, PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa ta gano Asusun Najeriya na Waje saura dala biliyan 15 kacal a cikin sa, ba dala biliyan 36 da CBN ya yi iƙirari sun rage a ciki ba.
Sannan kuma Najeriya ta kashe dala biliyan 5.9 wajen shigo da kaya tsakanin Janairu zuwa Afrilu kaɗai.
Haka kuma an gano cewa Asusun Rarar Kuɗin Fetur ya ƙafe ƙarƙaf, daga dala miliyan 35.37 ya koma saura dala 376,655 kaɗai.
Sannan kuma kuɗin da Najeriya ta samu tsakanin Janairu zuwa Afrilu bai wuce naira tiriliyan 1.63 ba, amma a cikin watannin an biya bashin naira tiriliyan 1.94. Kenan an samu giɓi na naira biliyan 300.
Gwamnonin Najeriya na so Gwamnatin Buhari ta gaggauta cire tallafin mai, kuma a rage kuɗaɗen da ake kashewa wajen ayyukan inganta rayuwa.
Sun kuma nemi a daina bai wa ‘Yan Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya ayyukan raya ƙasa.
Gwamnonin Najeriya sun nemi a rage kuɗaɗen da ake kashe wa ma’aikatan hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya. Kuma a sayar da masana’anta mallakar gwamnati, wadda ba wata tsayayyar kadara gare ta ba.
Haka nan kuma Gwamnonin Najeriya sun nemi a dakatar da shirin ƙara wa ma’aikata albashi kashi 22% da ake shirin yi cikin 2023.
Sun kuma nemi ma’aikatan gwamnatin tarayya su daina fita waje. Kuma Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta yana biza ga ma’aikata da iyalan su, sai da amincewar Fadar Shugaban Ƙasa.
Da su ka juya kan haraji kuwa, Gwamnonin Najeriya sun nemi a ƙirƙiro Harajin Saye da Sayarwa na 10% a kowace jiha da Abuja.
Kuma su na so duk mai samun naira 30,000 a wata, to a danƙara masa harajin biyan kashi 3% na kuɗin da y samu.
Waɗanda abin da su ke samu a wata bai kai naira 30,000 ba kuwa, su kuma ƙaƙaba masu harajin naira 100 duk wata kawai.
Gwamnonin na so a riƙa tattarawa da killace kuɗaɗen harajin mai da waɗanda ba na mai ba a wuri ɗaya. Kuma sun nemi a gaggauta ƙara yawan ɗanyen man da ake haƙowa.
A ƙarshen sun bayar da shawarar Gwamnatin Tarayya ta taimaka da kuɗaɗe idan akwai buƙatar hakan, domin ganin an kammala ginin Matatar Fetur ta Ɗangote, domin a riƙa tace fetur cikin gida Najeriya.
Sun ce yin haka zai sa Najeriya ta daina kwasan dibiliyon daloli ta na fita waje da su.
Discussion about this post