Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana ƙorafin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa a NNPP, Rabi’u Kwankwaso ya yaudare shi, shi da mutanen sa, ya sa zai fice ya koma wata jam’iyyar.
Shekarau ya ce Kwankwaso ya karya alƙawurran da ya ƙulla tare da shi, kafin ya rungumi sauran magoya bayan sa su fice daga APC zuwa NNPP a cikin Mayu, 2022.
Shekarau ya ce baya shi da aka bai wa takarar sanatan shiyyar Kano ta Tsakiya, wadda a yanzu dama a kan ta ya ke, babu wani makusancin sa da aka bai wa takara.
A wata tattaunawa da BBC Hausa ta yi da Kwankwaso, tsohon Gwamnan Kano ɗin shi kuma cewa ya yi “Shekarau ya bijiro da sharuɗɗan buƙatun abin da ya ke so a yi wa tawagar sa ɗin a makare. Saboda a lokacin kwanakin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta rufe lokacin sauya sunayen ‘yan takara.
“Kuma a siyasa, ya kamata ka sani cewa abu ne mai wahala ka ce wa wani ɗan takara ya janye ya bar wa wani, kuma ya amince da haka ɗin.”
Sai dai kuma Shekarau ya ce tun a ranar 16 Ga Mayu aka naɗa kwamiti, amma bai yi aikin sa ba, ya riƙa ɓata lokaci.
“A ranar 19 Ga Mayu kuma NNPP ta fitar da sunayen ‘yan takara, amma babu sunayen ‘yan tawaga ta waɗanda su ka biyo ni cikin NNPP daga APC. Na garzaya Abuja na samu Kwankwaso, na kuma kira Shugaban NNPP na Ƙasa. Aka ce an bar mana takarar kujerar majalisar tarayya 13 ta jiha kuma 31.”
PREMIUM TIMES Hausa ta tuna yadda Kamawa su ka riƙa bayyana ra’ayin su a lokacin da Shekarau a ya haɗe da Kwankwaso a siyasance.
“Ni ba zan taɓa amincewa da Shekarau ba, har sai ranar zaɓe ta zo na tabbatar da cewa NNPP ce ya dangwala wa ƙuri’a. Sannan zan yarda da shi.” Inji wani suna Aliyu.
“Kwankwaso da Shekarau ba za su taɓa zama inuwa ɗaya ba a siyasance. Ko sun zauna, ɗaya zai tashi ya bar ɗayan a wurin.” Cewar mutane da dama.
Waiwayen Baya A Siyasar Kano: Guguwar Da Ta Watsa Shekarau Cikin NNPP:
Makonni biyu kafin zaɓen fidda-gwanin ‘yan takara a Najeriya, bishiyoyin jam’iyyar PDP da APC sun yi yaushi a Kano, sakamakon gatarin da jam’iyyar NNPP ta yi amfani da shi ta sare rassan PDP, sannan ta tsallaka cikin gonar APC ta jijjige bishiyar.
Kusan za a ce APC da PDP a Kano dai sun yi yaushin da ko an shekara ana zuba masu ruwa, bishiyoyin biyu ba za su sake tohon sabon ganye ba.
Jam’iyyar NNPP wadda ba a sani ba kafin jagoran Kwankwasiyya Rabi’u Kwankwaso ya shiga jam’iyyar, a yanzu ta zama abin tsoro a Kano, jihar da ta fi sauran jihohin Najeriya yawan masu jefa ƙuri’a. Kuma jihar da kowane ɗan takarar shugaban ƙasa ke tsananin ya lashe a lokacin zaɓe.
Shi kan sa uban jam’iyyar NNPP ya yi mamakin ganin yadda jam’iyyar ta yi saurin samun tagomashi a Arewacin Najeriya. Dalili kenan ya rasa ta cewa, sai ya ce “wannan kuma wata mu’ujiza ce daga Ubangiji kawai.” Haka Boniface Aneboanam ya furta.
Ba wani abu ya yi saurin ƙara wa NNPP ƙarfi a Kano ba, sai gagarimin rikicin da ya tirniƙe PDP mai adawa da kuma APC Mai mulki a jihar.
Kwankwaso ya fice daga APC bayan da aka sake naɗa Abdullahi Abbas shugabancin jam’iyyar APC.
Sannan kuma rikicin cikin gidan PDP da su Wali ya sa Kwankwaso ficewa daga PDP.
A wani ɓangare can kuma APC na fama da na ta rikice-rikicen a Kano, biyo bayan ƙaƙaba Mataimakin Gwamna Nasiru Gawuna da Gwamna Ganduje ya yi, a matsayin wanda zai yi takarar gwamna a APCin Kano a zaɓen 2023.
Dama tun a wurin zaɓen shugabannin jam’iyya an samu mummunar ɓaraka a tsakanin ɓangaren Abdullahi Abbas wanda Gwamna Ganduje ke mara wa baya da kuma ɓangaren Haruna Ɗanzago, wanda Sanata Shekarau da Sanata Barau Jibrin ke mara wa baya.
Bayan zaɓe an ci gaba da shari’a har zuwa Kotun Ƙoli, inda aka bai wa ɓangaren Abdullahi Abbas rinjaye.
Wannan ya kawo ɓarkewar APC inda manyan ‘yan jam’iyyar su ka yi ta tururuwa cikin NNPP.
Guguwar ‘Fecewar’ ‘Yan APC Zuwa NNPP A Kano:
Jiga-jigan APC, ‘Yan Majalisar Tarayya da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati sun saki Ganduje sun kama Kwankwaso a NNPP.
Yayin da guguwar sauyin sheƙa ta murtuke jam’iyyar APC a Kano, har ta hana Gwamna Abdullahi Ganduje barci mai nauyi, yanzu kuma wasu manya kuma jiga-jigan gwamnati da jam’iyya sun ƙara ficewa daga APC a Kano, su na komawa NNPP, jam’iyyar Kwankwaso.
‘Yan Majalisar Tarayya biyu, Tijjani Joɓe da Badamasi Ayuba, tare da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Kano, Ali Makoɗa sun fice daga APC, sun koma NNPP.
Ficewar ta su dai ya tabbatar da cewa manyan ‘yan APC za su tsiyaye daga jam’iyyar su sauya sheƙa, biyo bayan yadda Gwamna Abdullahi Ganduje ya tsayar da Mataimakin Gwamna Nasiru Gawuna a matsayin ɗan takarar APC, yayin da Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, kuma zai yi masa mataimaki a takarar zaɓen 2023.
Sauran waɗanda su ka fice ɗin sun haɗa da Ahmed Muhammadu, Mai Binciken Kuɗi na APC na Jihar Kano; Umar Maitsidau, Shugaban Matasan APC na Kano, kuma tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Makodai da kuma wasu fitattu a siyasar Kano.
Dama kuma tsohon Kakakin Majalisar Kano, wanda a yanzu Ɗan Majalisar Tarayya ne, Alhassan Rurum da Kawu Sumaila da Aminu Garo, duk sun fice daga APC.
Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati Ali Makoɗa dama ya aika wa Gwamna takardar ajiye aiki domin ya tsaya takara, amma sai Ganduje ya shawarci shi ya ci gaba da aikin sa, ya ƙi karɓar takardar ajiye aikin da ya aika masa.
Amma a ranar Juma’a ya tabbatar da ajiye aikin sa, kuma ya shaida cewa ya koma NNPP.
Ɗan Majalisar Tarayya Tijjani Joɓe ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ya fice daga APC zuwa NNPP, domin ci gaba da samar wa al’ummar Mazaɓar sa ayyukan inganta rayuwa.
Discussion about this post