A ranar Talata ce Gwamnatin Najeriya ta sa hannun wata sabuwar yarjejeniya da Gwamnatin Amurka, inda za a maido wa Najeriya dala miliyan 23 da aka sace daga ƙasar nan, aka ɓoye a can tun zamanin mulkin Abacha.
Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya wakilci Najeriya wurin sa hannun yarjejeniyar wadda aka ƙulla a Ma’aikatar Harkokin Shari’a ta Tarayya, ranar Talata, a Abuja.
Yayin da Jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Leonard ce ta wakilci Amurka, kuma ta sa hannu a madadin ƙasar.
Ta bayyana cewa kafin wannan dala miliyan 23, cikin 2020 ma Amirka ta maido wa Najeriya dala miliyan 311.7 duk irin kuɗin da ɓarayin gwamnati su ka sace su ka kimshe a waje zamanin mulkin Abacha.
Malami ya ce kuɗaɗen na daga cikin irin kuɗaɗen da Najeriya ta yi yarjejeniyar a maido mata ne, tsakanin ta da Amurka da Birtaniya.
“Ina so a sani cewa kamar yadda ya ke a cikin yarjejeniyar, tuni har Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba amincewa za a yi amfani da kuɗaɗen wajen ci gaba da Ayyukan Raya Ƙasa na Ofishin Shugaban Ƙasa, wato PIDF da su ka haɗa da ci gaba da ayyukan titin Abuja zuwa Kano, ƙarasa titin Legas zuwa Ibadan da ci gaba da aikin Gadar Kogin Neja, waɗanda ake yi a ƙarƙashin NSIA.
“Nauyin da Shugaban Ƙasa ya ɗora min shi ne na tabbatar cewa dukkan kuɗaɗen satar da aka karɓo daga ƙasashen waje an yi aiki da su bisa sa idon ƙungiyoyin rajin kare haƙƙin jama’a, domin a kammala ayyukan nan muhimmai guda uku a cikin lokacin da aka ƙayyade za a kammala ayyukan.” Cewar Malami.
Discussion about this post