A ranar Laraba ce Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke kwaskwarimar da Antoni Janar Abubakar Malami ya yi wa Sharuɗɗa da Ƙa’idojin Aikin Ƙwararrun Lauyoyi a Najeriya.
Malami dai shi kaɗai ya yi gabagaɗin yi wa dokokin (RPC) kwaskwarima cikin 2020.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA), Monday Ubani ne ya shigar da ƙarar, inda ya shaida wa kotu cewa Minista Abubakar Malami ya yi kaɗan da yi wa dokokin kwaskwarima.
Kwaskwarimar da Malami ya yi wa RPC ita ce cire tambari da sitamfi na sa hannun lauyoyi. Sannan kuma ya cire wurin da RPC ta ce “su ma lauyoyin da ke wakiltar gwamnati, ministoci or hukumomi da cibiyoyi tilas sai sun riƙa biyan kuɗin da sauran layoyi ke biya duk shekara.”
A ƙa’ida, ana buƙatar tambari da sitamfi kan duk takardun da lauyoyi su ka sa hannu domin amincewa da kwafen takardun.
Baya ga yin amfani da tambari da kuma sitamfi domin hana buga takardun lauyoyi na bogi, Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) na amfani da su a matsayin hanyar samun kuɗin shiga ga ƙungiyar.
Cire waɗannan ke da wuya sai lauyoyi su ka fara sukar Minista Malami, su ka riƙa zargin sa katsalandan ɗin kashe kaifi da ƙarfin NBA.
Wasu mambobin ƙungiyar lauyoyin sun fice daga NBA, su ka kafa sabuwar ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya, (NNBA), tare da zargin nuna masu bambanci da rashin kulawa kan kula da muradun msmbobin NBA da ake fama.
Amma a cikin ƙarar da Ubani tare da wasu lauyoyi irin su Okoro Nkem, Clement Chukwuemeka da sauran wasu bakwai su ka shigar, sun maka Malami kotu, su ka nemi a haramta wa Malami yi wa dokokin NBA kutse.
A hukuncin da ya yanke ranar Laraba, Mai Shari’a Donatus Okorowo ya ayyana cewa, “kwaskwarimar da Minista Malami ya yi haramtacciya ce, don haka ya soke ta.”
Mai Shari’a ya ce Malami ba shi da ƙarfin ikon yi wa sharuɗɗan gyare-gyare ko cire wasu.
Ya ce ai mambobin mutane ne daban-daban su ka haɗu su ka gindaya sharuddan. Don haka haram ne wani mutum shi kaɗai ziƙau.
Shekaru biyu kenan da shigar da ƙarar, amma dai a ranar Laraba kotu ta yanke hukunci.
Discussion about this post