Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta dakatar da Shugaba Muhammadu Buhari da Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labarai ta Najeriya soke lasisin wasu kafafen yaɗa labarai 53 na ƙasar nan.
Gwamnatin Buhari da NBC sun soke lasisin na su ne bisa dalilin cewa sun ƙi zuwa su sabunta lasisin na su.
Mai Shari’a Akintayo Aluko ne ya yanke wannan hukuncin wucin-gadi, inda ya bada umarnin kada a sake a rufe gidajen radiyo da talabijin ɗin.
Ƙungiyar rajin kare haƙƙin jama’a mai bin diddigin tabbatar da komai kan ƙa’ida, wato SERAP da kuma Ƙungiyar Editoci ta Najeriya (NGE) ne su ka garzaya kotu, su ka ƙalubalanci wannan shiri da NBC ta yi na ƙoƙarin kulle gidajen rediyo da talabijin ɗin.
A ranar Litinin ce SERAP ta wallafa tare da watsa bayanan hukuncin da kotun ta yanke. Babban jami’in ta mai suna Kolawole Oluwadare ne ya watsa, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin ɗin.
Sanarwar ta ce Mai Shari’a ya ce a koma kotu a ranar 8 Ga Satumba, domin a ci gaba da sauraren ƙorafin da SERAP da NGE su ka gabatar a gaban sa.
Wannan kwanaki za su bai wa NBC da Buhari damar kare kan su da kuma bayyana dalilin da ya sa su ka soke lasisin tashoshin. Sannan kuma NBC da Buhari na da ikon ƙalubalantar hukuncin da kotun ta yanke, idan su na da ƙwaƙƙwarar madogara.
Idan ba a manta ba dai a ranar 19 Ga Agusta ce NBC ta bayyana soke lasisin tashoshin radiyo da talabijin 53.
Gwamanti ta ce sun ƙi sabunta lasisin su, wanda adadin kuɗin da tashoshin ya kamata su biya, idan an haɗa su za su kai naira biliyan 2.66.
NBC ta bayar da umarnin duk tashar da ba ta biya ba, to ta kulle gabatar da shirye-shiryen ta ƙarfe 12 na dare, a ranar 20 Ga Agusta.
Discussion about this post