Wani bincike da wata jaridar yanar gizo a Amurka mai suna INTERCEPT ta gudanar, ta zargi Amurka da taka rawa a harin da Sojojin Sama na Najeriya su ka kai Sansanin Gudun Hijira da ke ƙauyen Rann a Jihar Barno.
Cikin 2017 ne Sojojin Saman Najeriya su ka jefa bam a sansanin wanda ya kashe sama da mutum 160, waɗanda yawancin su ƙananan yara ne.
Rahoton da INTERCEPT ta buga a ranar 28 Ga Yuli ɗin nan, ya nuna Amurka na da hannu wajen tsara yadda za a kai harin. Sai dai kuma an kai harin ne a bisa kuskure, yayin da aka yi tsammanin sansanin ‘yan Boko Haram ne, ba sansanin gudun hijira ba.
“Hujjoji sun nuna Amurka ta yi wani gagarimin bincike na cikin gida, saboda ita ce ta bayar da rahoton sirri cewa ‘yan Boko Haram ne a wurin.”
Jaridar ta bada labari da kuma kafa hujja da wasu bayanan sirri na Sojojin Amurka da su ka faɗo hannun ta.
“An shirya gudanar da binciken ne wanda wani babban jami’in sojan Amurka da ke lura da dakarun Amurka da aka girke Afrika ya bayar da umarnin a gudanar, don kawai a kauce wa hukunta wasu.”
PREMIUM TIMES tun a 2017 ɗin ta buga labarin wanda a cikin Janairu 2017 aka kai harin bam a sansanin da aka yi tsammanin na Boko Haram ne.
Sojojin Najeriya da Gwamnatin Tarayya sun ce jirgin yaƙin ya yi nufin kai wa Boko Haram harin bam ne, amma a bisa kuskure aka jefa bam ɗin kan masu gudun hijira a sansanin Rann.”
“Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta yi nadama, inda a harin bam ɗin bayan kashe mutum 160, cikin su 9 ma’aikatan agaji ne, wasu 120 kuma sun ji munanan raunuka.”
“Yayin da aka lura da gilmawar mutane da yawa a yankin, sai na’urar satilayit daga nesa ta nuna Boko Haram ne a wajen, waɗanda kuma aka nuna ana buƙatar kakkaɓe su da gaggawa.” Haka Kakakin Hukumar Tsaro ta Sojoji John Eneche ya bayyana a lokacin.
Ya ce a lokacin Sansanin Gudun Hijira na Rann ba ya cikin lissafin sansanonin da ke Jihar Barno, shi ya sa ba ya cikin lissafin waɗanda aka sani.”
Rahoton dai ya ce Amurka ce ta yi leƙen asirin gano cewa ‘yan Boko Haram ne a wurin, kuma ta sha bada rahotannin asiri da dama.
Jaridar INTERCEPT ta ce Rundunar Sojojin AFRICOM ba ta amsa mata tambayoyin ta ba kan sakamakon binciken Stoke ko irin rawar da Amirka ta taka.”
Sai dai kuma Amurka ta ƙaryata zargin ta da hannun a harin bam ɗin da jirgin yaƙin Najeriya ya kashe fiye da mutum 160 ya raunata 120 a cikin 2017, a sansanin Rann, Jihar Barno.
Jeanne Clark wadda ita ce Kakakin Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya, ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba aikin Amurka ba ne kai hare-hare a Najeriya. Sojojin Najeriya ne ke kai farmakin da kan su, domin a tabbatar da ba a kai hari inda ba can ya kamata a kai ba.
Ba wannan ne kaɗai wurin da Sojojin Saman Najeriya su ka taɓa jefa bam a kan kuskure ba.
A ranar 5 Ga Satumba, 2021, sojojin saman Najeriya ta buɗe wa fararen hula wuta a Jihar Yobe.
Bayan kai harin da makonni biyu kuma sai Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta ɗauki alhakin buɗe wa fararen hula wuta a Ƙauyen Buhari, Jihar Yobe.
A ƙarshe dai Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta bayyana cewa ita ke da alhakin kai hari ta sama da jirgin yaƙi, a Ƙauyen Buhari, wanda ke cikin Ƙaramar Hukumar Yunusari a Jihar Yobe.
Harin wanda aka kai a ranar Laraba, an ce ya yi sanadiyyar kashe mutum 10 tare da jikkata mutum sama da 20.
Majiyoyi daga cikin yankin dai sun ce Sojojin Saman Jamhuriyar Nijar ne su ka kai harin wurin ƙoƙarin fatattakar wasu ‘yan Boko Haram.
Da farko kuma Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta nesanta kan ta da kai harin wanda aka buɗe wa fararen hula wuta a ƙwauyen.
“Ƙarya ake mana, ba Sojojin Saman Najeriya su ka kai harin ba. Rabon da Sojojin Sama su yi wani farmaki a Yobe tun a ranar 5 Ga Satumba, 2021.” Haka Kakakin Rundunar Sojojin Saman Najeriya, Edward Gabkwet ya bayyana a ranar Laraba
Sai dai kuma sa’o’i 24 daga baya, Rundunar Sojojin Saman ta yi amai ta lashe, inda ta fito ta bayyana cewa Sojojin Saman Najeriya ne su ka kai farmakin a bisa kuskure, kamar yadda Gabkwet ɗin ya sake bayyanawa daga baya.
Ya ce lamarin ya faru ne bayan da su ka samu rahoton gilmawar wasu ‘yan Boko Haram a kan gaɓar Kogin Kamadougou.
“Daga nan Sojojin Saman Najeriya su ka rufa su a kan iyakar Najeriya da Nijar a ranar 15 Ga Satumba, 2021.
Sanarwar ta ce an kashe fararen hula a kan kuskure ne.
Idan ba a manta ba, shekaru uku da su ka wuce, Sojojin Saman Najeriya sun yi ruwan wuta daga a kan Sansanin ‘Yan Gudun Hijira a Rann, cikin Jihar Barno, inda su kashe sama da mutum 260.
A wannan karo kuma, bayan Rundunar Sojojin Najeriya ta nesanta kan ta da kai farmakin a Yunusari, Premium Times ta bada labarin yadda Sojojin Jamhuriyar Nijar su ka afka wa mutanen ƙauyen Buhari da kisa bisa kuskure a Jihar Yobe.
An tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 10 tare da jikkata wasu mutum 20 a harin da Sojojin Jamhuriyar Nijar su ka kai wa ƙauyen Buhari.
Ƙauyen Buhari dai wani gari ne da ke da tazarar kilomita 20 daga Kananmma, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Yunusari ta Jihar Yobe.
Lamarin ya faru ne yayin da rahotanni su ka ce Sojojin Nijar sun afka garin ne lokacin da su ke farautar wasu ‘yan Boko Haram.
An kai harin ne jirgin yaƙi, inda aka kashe mutane da kuma jikkata wasu.
Ƙaramar Hukumar Yunusari na kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Ganau ya ce da idon sa ya ga motoci uku ƙirar Toyota Hilux ɗauke da waɗanda aka ji wa rauni an shiga da su Babban Asibitin Geidam.
Wata majiya kuma ta tabbatar da cewa an garzaya da wasu Babban Asibitin Gashua.
Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da lamarin, kuma yanzu haka Sojojin Najeriya sun kewaye garin, sun hana jami’an tsaro shiga, cikin waɗanda aka hana ɗin kuwa har da ‘yan sanda.
Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Yobe, Dungus Abdulkarim ya ce ba su da cikakken bayanin haƙiƙanin abin da ya faru a zuwa lokacin da aka tuntuɓe shi.
A na sa ɓangaren, Gwamnan Yobe Mai Mala-Buni ya umarci asibitocin Geidam, Gashua da Damaturu su kula da lafiyar waɗanda aka jikkata a farmakin Ƙauyen Buhari kyauta.
Haka nan kuma ya umarci Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe ta gaggauta tura kayan tallafi ga jama’ar ƙauyen da abin ya shafa.
Sannan kuma ya bada umarnin jami’an gwamnati su yi aiki tare da jami’an sojoji domin a gano musabbabin farmakin.
Buni ya miƙa ta’aziyya da jaje da alhini dangane da wannan mummunan hari.
Discussion about this post