Hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa, NBC ta soke lasisin tashoshin yada labarai 52 saboda kin sabonta lasisin tashoshin.
Hukmar ta ba su awa 24 su daina watsa labarai.
Manyan kamfanoni da suka yi fice a cikin jerin tashoshin da aka soke lasisin su sun hada da AIT, Silverbird dake da rassa a jihohi sama da biyan a fadin kasar nan. Sannan kuma a kawai tashar KSMC ta jihar Kaduna wanda ita ma ta fada cikin tashoshin da aka soke lasisin su.
Ko da yake mafi yawa daga cikin tashoshin da aka soke lasisin su masu zaman kansu ne, akwai da yawa wanda mallakin gwamnatocin jihohin kasar nan ne musamman Arewa.
Hukumar tace tun a watan Mayu ta ke ta yi wa masu mallakin tashohin tunin su gaggauta garzayowa ofishin hukumar su sabonta lasisin su su kuma biya dimbin basukan da ake bin su amma suka ki.
Discussion about this post