Shahararren yar wasan finafinan Hausa kuma mawaƙiya Safiya Yusuf wacce aka fi sani da Safara’u ta bayyana cewa mata da dama suna ɗaukan kansu tsirara su ajiye a cikin wayoyin su.
Safara’u ta bayyana haka a hira da ta yi da BBC Hausa inda ta yi magana kan yadda ta ji a lokacin da aka fidda bidiyon tsiraicinta ya karaɗe shafukan soshiyal midiya.
Jarumar ta ce ba za ta iya faɗi ko sanin wanda ya saka bidiyon a yanar gizo ba.
” Waya ta ta kowa ce, ina ba mutane su yi amfani da ita wayar kuma ciki akwai bidiyoyin tsiraici na da yawa a ciki wanda nake ɗauka don nishaɗi in rika kallo. Shine aka cire wannan bidiyo aka yaɗa shi a shafukan sada zumunta.
Ta ce ko da aka gaya mata cewa ga bidiyon nan yana tashe a yanar gizo bata ji daɗi ba.
” Na samu tsangwama matuƙa sannan kuma ban ji daɗin abinda ya faru ba. Sai dai iyaye na basu muzguna min ba sun tausasa ni ne suka rika cewa in kwantar da hannu na.
” A harkar nishaɗantarwa kuwa buri na shine a ce yau na zama kamar Davido ko Burna Boy. In rika rangaɗa waka ina samun kyaututtuka kara waɗannan fitattun mawaka.
Discussion about this post