A wani abu mai kama da cinikin biri a sama, Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ta bayyana cewa babu tsimi ba dabara Gwamnatin Tarayya za ta ciwo wani sabon bashi na naira tiriliyan 11 cur domin antaya kuɗaɗen ciki kasafin kuɗin 2023.
Ba a nan lamarin ya tsaya ba, Zainab ta ce kuma Gwamnatin Tarayya za ta sayar da wasu kadarorin gwamnati duk don a samu kuɗaɗen da za a yi ayyukan kasafin 2023 da su.
“Idan gwamnatin tarayya ta ci gaba da biyan tallafin fetur daga farko har zuwa ƙarshen 2023, to za a samu giɓin naira tiriliyan 12.42 a cikin kasafin kenan.
Zainab ta yi wannan magana yayin da ta bayyana a gaban Kwamitin Harkokin Kuɗaɗe na Majalisar Tarayya, lokacin da ta ke kare hassshen kuɗaɗen da gwamnati za ta kashe cikin shekarun 2023-2025, (MTEF).
Kasafin 2023: Gaba Kura Baya Siyaki:
Zainab ta je wa ‘yan Majalisa zaɓi guda biyu, kuma kowane babu mai sauƙi a cikin su.
Na ɗaya ta ce ki dai a ci gaba da biyan kuɗaɗen tallafin fetur, amma kuma a ƙarshen shekara ta 2023 a yi asarar naira tiriliyan 12.41 da za a samu giɓin su a cikin kasafin kuɗi, saboda za ta biya tallafin fetur har naira tiriliyan 6.72.
Zainab ta ce zaɓi na biyu kuma shi ne a ci gaba da biyan tallafin fetur har zuwa cikin watan Yuni, 2023, wanda hakan zai haifar da giɓin naira tiriliyan 11:30, saboda naira tiriliyan 3.3 kenan duk a biyan tallafi za su zurare.
Ta ce shawara ta farko ba lallai ba ne ta yi aiki, domin wahalar da ke tattare da tsarin. Na biyu kuma zai iya yiwuwa, amma sai gwamnati ta tsuke aljihu, kuma ta matsa ƙaimi kan kamfanoni da masana’antu na gwamnatin tarayya a cikin 2023.
Discussion about this post