Kotun daukaka kara a jihar Kano ya bada umarnin a sake shari’ar Aminu Yahaya-Sharif mawakin da aka yanke wa hukuncin kisa a dalilin kalaman batanci da yayi a wakar sa.
Alkalan kotun da suka yanke hukuncin a sake shari’ar Nuraddeen Umar, da Nasiru Saminu sun ce akwai matsaloli a cikin hukuncin da kotun shari’a ta yanke.
A sanadiyyar wannan waka da ya saki wanda akwai kalaman batanci ga Annabi, matasa sun fusa a wancan lokacin suka kone gidan iyayen sa a cikin birnin Kano.
Discussion about this post