Wani magidanci mai suna Isma’il Ibrahim ya maka sirikansa Zainab Muhammad a kotun shari’a dake Rigasa a jihar Kaduna saboda ta hana ta dawowa gida bayan ta shafe watanni uku a gidan iyayenta.
Ibrahim Wanda ke zama a hanyar ofishin ‘yan sanda dake Rigasa ya ce Zainab ta hana matarsa dawowa gida saboda shi ba mai arziki bane.
Ya ce yana kaunar matarsa sannan yana so ta dawo gida wurinsa.
“Ina rokon kotu ta taimaka wajen dawo mini da mata ta gida.
Zainab ta ce ta hana ‘yarta dawowa dakin mijinta ne saboda rashin kula da baya yi mata.
Zainab ta ce a tsakanin wannan lokaci ‘yarta ta yi rashin lafiya amma ibrahim bai iya biyan kudin asibiti ba.
“Bayan na biya kudin magani da asibiti Ibrahim ya bar ni da kula da ‘yata a gida.
Ta ce ta hana ta komawa gida ne saboda tana so ta zauna da ita har sai ta yi watanni 6 ta tabbatar ta warke sarai tukunna.
“Matar Ibrahim za ta dawo gida idan Ibrahim ya biya ni kudaden da na kashe na asibiti da wanda na kashe wajen ciyar da matarsa na tsawon watanni 9.
Alkalin kotun Malam Abubakar Salisu-Tureta ya daga shari’an zuwa ranar 4 ga Satumba domin Zainab ta gabatar da jimlar kudaden da ta kashe.
Discussion about this post