A rahoton da MICS da UNICEF suka bayar game da kaciyar mata a Najeriya, jihohin Kwara da Ekiti ne ke kan gaba wajen yi wa mata kaciya a najeriya.
Rahoton ya nuna daga shekarar 2016 zuwa 2021 jihar Kwara ta yi wa mata kashi 58% kaciya sannan jihar Ekiti ta yi wa mata kashi 50% kaciya a Najeriya.
Rahoton ya nuna cewa an samu karuwa a yawan mata musamman masu shekara 15 zuwa 49 da ake wa kaciya a Najeriya daga kashi 15% zuwa kashi 18% a shekarar 2016.
Sannan aka samu karuwa na kashi 25% daga kashi 8% a mata masu shekaru 0 zuwa 14 da aka yi wa kaciya a shekarar 2016.
Rahoton ya nuna jihohin Zamfara da Gombe na daga cikin jihohin da suka fi karancin yawan matan da aka yi wa kaciya a Najeriya.
An gabatar da wannan rahoto ne a ranar Talata a wurin taron gabatar da sakamakon binciken yin allurar rigakafi wanda Mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbanjo ya gabatar wanda ministan kudi Zainab Ahmed ta wakilta.
Yi wa mata kaciya a Najeriya
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa yi wa mace kaciya ya hada yanke wani bangare na gaban mace.
Sakamakon binciken da ma’aikatar harkokin mata ta gudanar kafin shekarar 2016 wanda UNFPA ta wallafa a shekaran 2021 ya nuna cewa an yi wa mata miliyan 19.9 kaciya a Najeriya daga shekarun 2004 zuwa 2015.
A dalilin haka Najeriya ta zama ƙasa ta uku a jerin kasashen da suka fi yi wa mata kaciya a duniya.
Kasar Masar ce ƙasa ta farko a jarein kasashen duniyan da suka fi yi wa mata kaciya inda a kasan an yi wa mata miliyan 27.2 kaciya.
Daga nan sai kasar Ethiopia da ta yi wa mata miliyan 23.8 kaciya sannan sai Najeriya da ta yi wa mata miliyan 19.9 kaciya.
Yarbawa, Hausawa, Kanuri, Fulani, Igbo da Ijaw na daga cikin kabilun da suka fi yi wa mata kaciya a Najeriya.
Daga cikin su kabilar Kanuri ce ta fi karancin yawan matan da ta yi wa kaciya a kasar nan.
Illoli shida dake tattare da yi wa mace kaciya
1. Hana mace jin dadin jima’i.
2. Hana haihuwa.
3. Kamuwa da cututtuka irin na sanyi da yake kama gaban mace.
4. Kawo zuban jini wajen haihuwa wanda ka iya kawo ajalin mace.
5. Kawo laulayin haila
6. kawo doguwar nakudar haihuwa
Discussion about this post