A kauyen Ode dake karamar hukumar Remo ta Arewa jihar Ogun ‘yan sanda sun cafke Amoda Bola mahaifin da ya dirka wa ‘yarsa mai shekaru 14 ciki.
Ƴan sandan sun kama Bola mai shekaru 49 a gidansa dake Idi Oro kauyen Ode bayan ƴar ta sa ta kawo kara ofishin ‘yan sanda.
Kakakin rundunar Abimbola Oyeyemi, ya ce yarinyar ta sanar wa ‘yan sanda cewa mahaifinta Bola ya dade yana lalata da ita sannnan kuma bai tsaya a nan ba kawai, ya kan gayyaci wasu mazajen suna lalata da ƴar ta sa suna biyan sa.
Oyeyemi ya ce rundunar ta kama Bola tare da wasu mutane da suka rika yin lalata da yarinyar.
Ya ce rundunar ta kama Ahmed Ogunkoya mai shekaru 30, Muyiwa Adeoye dan shekara 48, David Sunday Solaja mai shekaru 69, Emmanuel Olusanya Dan shekara 50 da Joshua Olaniran mai shekaru 50 da laifin aikata wannan lalata.
“Rundunar ta kama mahaifin da ya rika lalata da ‘yar cikinsa mai shekaru 14 tare da mai da ita karuwa baya ya rabu da mahaifiyarta.
“Sakamakon gwaje-gwajen da aka yi wa yarinyar ya nuna cewa tana da ciki sannan ita yarinyar ta tabbatar cewa mahaifinta ne ya dirka mata cikin saboda shi kadai ne ya rika lalata da ita a lokacin da ta yi cikin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bada umurin kai karar fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka domin ci gaba da bincike.
Oyeyemi ya ce da zarar rundunar ta kammala binciken ta za ta maka wadannan mutane a kotu.
Discussion about this post