Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi sun kama Munkaila Ado mai shekara 27 dake aiki a gidan Danladi Mohammed a kauyen Mai’ari Arewa dake karamar hukumar Alkaleri da laifin dirka wa ‘yar gidan da yake aiki ciki bayannan kuma ya kashe ta.
Daily Post wacce ta buga labarin ta ce Ado ya kashe yarinyar mai shekara 13 dake dauke da cikin wata hudu bayan ya hada baki da mahaifiyar yarinyar ya kai ta jihar Gombe domin a zubar da cikin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Ahmed Wakil ya ce rundunar ta samu labarin abin dake faruwa a lokacin da mahaifin yarinyar Danladi Mohammed ya shigar da kara a ofishinsu dake Mai’ari Arewa ranar 10 ga Agusta.
“Mohammed ya ce ‘yarsa Safiya tun da ta bar gida ranar 4 ga Agusta ba ta dawo gida ba.
” Mahaifin ya ce yana zargin yaron dake masa aiki Ado da abokinsa Muazu Umaru mai shekara 35 na da hannu a bacewarta.
Ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa Ado da abokinsa sun kashe Safiya bayan an zubar da cikin, suka kona gawan ta sannan suka haka rami mara zurfi suka rufe ta a ciki a wani daji dake karamar hukumar Akko a jihar Gombe.
“Mun Kuma gano cewa Ado ya kai Safiya gidan wata Hajiya Amina Abubakar mai shekaru 50 a Jekada Fari dake bayan asibitin FMC Gombe aka cire mata cikin.
Wakil ya ce rundunar ta kama Ado da Umar bisa laifin tauye hakki Safiya da cin zarafinta.
Bayan haka rundunar ta kama wani Alhamdu Yusuf mai shekaru 59 da ake masa zargin aikata laifin yi wa ‘yar wata 18 fyade a Yelwan Kagadama dake jihar Bauchi.
Wakil ya ce mahaifiyar yarinyar Nenkat Danladi ce ta kawo kara ofishinsu dake Yelwa.
“Nenkat ta ce a ranar 9 ga Agusta da misalin karfe 7 na yamma ta iske Yusuf kwance a kan gadonta da ‘yarta.
“Ta ce bayan ta duba ‘yarta ne ta ga jini na fitowa daga gaban yarinyar.
Ya ce yarinyar na asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa likitoci na duba ta sannan Yusuf na tsare a ofishin su.
Discussion about this post