Gwamnatin Najeriya ta tabbatar cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da bayar da gudummawar naira biliyan 1.4 ga Jamhuriyar Nijar.
Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ta shaida wa manema labarai a ranar Laraba bayan tashi daga taron Majalisar Zartaswa a Fadar Shugaban Ƙasa cewa, an yi gudummawar ce domin sayen motocin da Nijar za ta inganta tsaro a cikin ƙasar ta.
Zainab cta ce ai irin wannan gudummawa ga maƙwautan ƙasashe ba baƙon abu ba ne ga Najeriya, an saba yin haka ɗin.
Ta ce Shugaban Ƙasa ne ke da ikon yin haka, bayan ya yi nazarin halin da ake ciki na damuwa kan ƙalubalen matsalar tsaro.
“Bari na faɗa maku, ai dama lokuta da dama Najeriya kan tallafa wa ƙasashen da ke maƙautaka da ita, musamman a fannin matsalar su wadda ta fi shafar mu.” Haka Zainab ta shaida wa manema labarai.
“Saboda haka ba wannan ne karo na farko da Najeriya ta taimaki Jamhuriyar Nijar, Kamaru ko Chadi ba.
“Shugaban Ƙasa ne da kan sa ya yi nazarin abin da ya kamata a yi, bisa buƙatun da shugabannin ƙasashen ke bijiro mana da su. Sai a amince, kuma a bayar da taimakon da su ke buƙata ɗin.
“An bayar ne domin su inganta matakan tsaro, domin matsalar tsaron su ta shafi Najeriya kai-tsaye.”
Zainab ta ce ita fa ta fahimci damuwar da ‘yan Najeriya ke nunawa game da kamfatar kuɗaɗe a miƙa wa Nijar, tun bayan da labarin ya ɓulla.
“Yan Najeriya na da ‘yancin yin tambaya, amma kuma shi ma Shugaban Ƙasa na da ƙarfin ikon yin nazarin abin da ke alfanu ga ƙasa. Don haka ni kuma ba ni da ikon cewa kada a yi, ko na tambayi me ya sa za a yi.” Inji Ministar Harkokin Kuɗaɗe.