Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa babban burin sa na fitowa takarar gwamnan Kaduna shine domin ya ɗanɗana wa talakan jihar Kaduna lagwadar siyasa har gida.
Ashiru wanda ya taba rike mukaman ɗan majalisa a majalisan jihar Kaduna na tsawon shekaru sannan ya rike kujerar ɗan majalisa a majalisar wakilai ta tarayya ya ce kwarewar sa a harkar mulki da yi wa talaka bauta ya sa yake ganin idan ya zama gwamna zai yi wa mutanen jihar Kaduna abin da ba a taba yi musu ba.
” Ko a harkar ilimi, a jihar Kaduna za mu gyara harkar ne ta yadda ba kawai karatu a littafi ƴaƴan mu za su yi ba, zaka yi karatu ne kana koyon sana’a.
” Haka kum maganar tsaro, zamu maida hankali matuka wajen hada kai da sarakuna domin samar da tsaro. Masu Unguwanni, Dagatai, Sarakuna na da amfani matuka a harkr samar da tsaro, zamu yi amfani da su wajen tsara harkar tsaro a jihar mu.
Isah Ashiru ya kara da cewa ” Ko a wurin harkar noma zan yi abinda ba a taba yi ba a jihar Kaduna. Manoman mu sa su rika yin noma ne sau uku a shekara, za mu bunƙasa noman rani ba da wasa ba.
A karshe ɗan takarar ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa bai taɓa jin kwanciyar hankali da yin nasara ba kamar yadda yake ji yanzu saboda su kan su mutane sun ji a jikin su
” Mutane sun ji a jikin su kuma sun dandana salon irin mulkin APC a jihar.
Discussion about this post