Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na dukkan bakin ƙoƙarin ganin sauran waɗanda ke hannun ‘yan ta’adda sun koma gidajen su lafiya.
Buhari ya yi wannan alwashin a ranar Alhamis, lokacin da wakilan waɗanda aka yi garkuwa da su, su ka kai masa ziyara a fadar sa.
Yayin da ya ke ta’aziyyar waɗanda su ka rasa rayukan su a lokacin harin da kuma jimamin halin da waɗanda ke tsare ke ciki, Buhari ce shi da ‘yan Najeriya sun taya su baƙin ciki da shiga halin damuwa ƙwarai da gaske.
Buhari ya shaida masu cewa bayan faruwar farmakin, gwamnati ta ɗauki matakai da dama domin samar wa iyalan su sauƙin damuwa da kuma tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ba.
Sannan kuma ya bayyana dalilin da ya sa ba a yi amfani da ƙarfin sojoji ba wajen kuɓutar da sauran waɗanda ke tsare ɗin.
“An faɗa min cewa a lissafin baya-bayan nan saura mutum 31 a hannun masu garkuwar. To kuma burin da mu ka sa gaba shi ne mu ga cewa su ma sauran mutum 31 ɗin duk sun koma wurin iyalan su.
“Mun fahimta a irin wannan mummunan yanayi dole damuwa ta ƙara yawa. Mun samu shawarwari da yawa dangane da yadda za a yi amfani da manyan makamai domin kuɓutar da sauran waɗanda ke tsare.
“To kowace hanyar da aka yi tunanin amfani da ita, ana duba yiwuwar hakan da abin da zai iya biyo bayan hakan.
“To sai dai kuma duk hanyar da aka so a bi, za a ga babu garanti ɗin kuɓutar da su a raye, ba tare da an rasa rayukan da yawan waɗanda ake tsare da su ɗin ba.
“To ni kuma babbar damuwa ta ita ce kowanen su ya samu kuɓuta da ran sa da lafiyar sa, ba tare da an raunata shi ba.” Inji Buhari.
Buhari ya ci gaba da ba su labarin irin ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen daƙile ta’addanci da hare-haren ‘yan bindiga.
Wakilin waɗanda ke tsaren da ya yi wa Buhari jawabi, mai suna Sabiu Mohammed, ya roƙi gwamnatin tarayya ta agaza wa iyalan sauran waɗanda ke tsare, domin a sako su.
“Mu na roƙo don Allah ta taimaka a sako sauran waɗanda ke hannun masu garkuwa ɗin. Iyalan su sun shiga cikin ruɗani da damuwa da halin ƙunci. Ba mu kuɗaɗen da masu garkuwar ke neman a biya su.
“Shugaban Ƙasa, mun san ka na bakin ƙoƙarin ka. Amma don Allah mu dai mu na son ganin ‘yan uwan mu da ke tsare.” Inji Sabiu Mohammed.
Discussion about this post