Kakakin fitaccen malamin addinin musulunci sheikh Ahmed Gumi, Tukur Mamu ya ce ba gaskiya bane da ake raderadin wai ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris sun saki duka sauran wadanda ke tsare a hannun .
Mamu wanda ke daya daga cikin mutanen da suka yi ruwa suka yi tsaki wajen ceto fasinjojin da maharan suka yi garkuwa da su ya ce har yanzu a kwai mutum 27 dake tsare a hannun maharan.
Ya ce maharan na sakin fasinjojin kashi-kashi ne kuma ma sai sun karbi kudin fansa daga ‘yan uwan su.
A ranar 10 ga Agusta ne maharan suka sako mutum 6 cikin fasinjojin. Cikin akwai wata mata mai shekaru sama da 60 wanda rashin lafiya ya mata tsanani, sai kuma dan tsohon gwamnan Kano da iyalan sa wanda kaf din su suna wannan jirgi ne a lokacin da aka yi garkuwa da mutanen ciki.
Mamu ya ce yana so ya tabbatar wa mutane cewa har yanzu akwai sauran fasinjojin dake tsare hannun ‘yan bindigan.
“Da dama daga cikin mutanen dake tsare a hannun ‘yan bindiga na fama da rashin lafiya.
Ya yi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya tsananin bada umarnin a saki sauran fasinjojin dake tsare.
Discussion about this post