Ministar Harakokin Kuɗaɗe, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed ta bayyana cewa Majalisar Zartaswa ta Ƙasa ta amince a shirya taron gangamin dukkan jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyi masu faɗa-a-ji, domin a tattauna yadda za a cimma matsayar yarjejeniyar a cire tallafin fetur.
Zainab ta bayyana haka ranar Alhamis a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya mai binciken yadda ake kashe kuɗaɗen tallafin fetur.
Sannan ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta yi shirin kashe naira tiriliyan 3.35 wajen biyan tallafin fetur a cikin 2023 daga Janairu zuwa ƙarshen Yuli na shekarar.
Minista Zainab ta ce tunanin a yi gangamin shawara a amincewar ɗaukar matsaya ɗaya kan cire tallafin fetur, batu ne shugabannin majalisar tarayya da ta dattawa su ka bayar shawara.
Daga nan ta ce yanzu haka har an fara tsare-tsaren shirya taron.
Ta ƙara da cewa gwamnatin tarayya na kashe naira biliyan 18 6 a kullum a ɓangaren fetur, kuma an kashe naira tiriliyan 6.2 wajen biyan tallafin fetur daga 2013 zuwa 201.
Ta ce a cikin watanni shidan ƙarshen wannan gwamnatin za ta kashe naira tiriliyan 3.35 wajen biyan kuɗaɗen tallafin fetur.
Zainab ta ce Gwamantin Tarayya na biyan naira 283.3 a kowace lita ɗaya ta fetur.
“Mun zauna da shugabannin majalisun ƙasa, sun bayar da shawarar me zai hana a yi taron masu ruwa da tsaki da su ka haɗa har da shugabannin jam’iyyun siyasa. Mun gabatar da wannan shawara ga Majalisar Zartaswa, kuma ta amince a fara shirin tsara taron.
“Akwai buƙatar yin wannan taro ya kasance tattaunawa ce ta ƙasa baki ɗaya. Idan ƙasa baki ɗaya ta amince a cire tallafin fetur, to sai a cire ɗin.
“Ba abu da Shugaban Ƙasa zai ce ga yadda za a yi ba. Ba ma’aikatar harkokin kuɗaɗe ce za ta bayar da shawarar yadda za a yi ba.” Inji Zainab.
Matsayar da aka cimma dai a yanzu ita ce, irin maƙudan kuɗaɗen da ake kashewa wajen biyan tallafin fetur, ba abu ne da zai iya ɗorewa ba.
Sannan ta ce gwamnatin tarayya ta damu ƙwarai ganin yadda a kullum cikin ƙasar nan ana sayen fetur har lita miliyan 64. Shi ya sa aka yanke shawarar cewa har gara kawai a cire tallafin fetur baki ɗaya.
Shugaban Kwamitin Bincike Ibrahim Aliyu mai wakiltar jihar Sokoto, ya ƙi yarda da adadin lita miliyan 64 da minista ta ce ana sha a Najeriya. Ya ce kawai dai ta zuguguta adadin ne dai.
“Cikin 2013 fa ƙididdiga ta nuna ana shan tila miliyan 31. Don haka zai yi wuya a ce adadin ya nunka a ciki shekaru 10.”
Daga nan ya shawarci minista ta dai sake lissafin da mai hankali zai iya fahimta har su ma su gamsu kuma su amince.
Discussion about this post