Ministan Harkokin Ilmi Adamu Adamu, ya bayyana cewa a cikin shekaru shida da su ka gabata, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kashe naira tiriliyan 6 a ɓangaren ilmi.
PREMIUM TIMES Hausa ta jinjina nauyin kuɗaɗen ta ji sun yi daidai da Kasafin Najeriya na shekara 2016 baki ɗaya.
A ranar 22 Ga Disamba, 2015, Shugaba Buhari ya yi bayanin Kasafin Shekara ta 2016 na tsabar kuɗi naira tiriliyan 6.08.
Baya ga naira tiriliyan 6 ɗin da Minista Adamu ya ce an kashe wa ɓangaren ilmi cikin shekaru 6, ya ce akwai ma ƙarin naira tiriliyan 2.5 da aka kashe a Hukumar Bunƙasa Ilmin Manyan Makarantu (TETFund).
Waɗannan kuɗaɗe su kuma daidai su ke da kashi 2 bisa 100 na adadin kuɗaɗen harajin kamfanonin Najeriya.
Sannan kuma akwai wasu kuɗaɗen da dai Ministan ya ce an narka a fannin ilmi, waɗanda ba su cikin waɗannan lissafe-lissafe da ke sama. Wato naira biliyan 554 a ɓangaren Hukumar UBEC, kamar yadda Adamu ya tabbatar.
Adamu wanda ya yi wannan bayani a taron ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, ya kuma taɓo sauran batutuwan da su ka shafi harkokin ilmi, waɗanda su ka haɗa da yajin aikin malaman jami’o’i da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.
Ya ce a cikin shekaru 10 an kashe wa ɓangaren ilmin manyan makarantu naira tiriliyan 2.5.
Ya ce wannan adadi ya ma ninka naira tiriliyan 1.2 ɗin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta buƙaci gwamnati ta kashe a ɓangaren ilmi, wanda sharaɗi ne da da ke cikin yarjejeniyar ASUU ta 2009.
Minista ya ce, “Gwamnatin Buhari ta kashe naira 6,003,947,848,237 a ɓangaren ilmi cikin shekaru bakwai.”
Ya ƙara da cewa UBEC ta kashe wa Ilmin Manyan Makarantu naira biliyan 553,134,967,498.
“Hukumar TETFund kuma ta kashe naira tiriliyan 2.5 a cikin shekaru 10. Kuɗaɗen sun ma haura ƙa’idar naira tiriliyan 1.2 da ASUU ta gindaya a riƙa kashe wa fannin ilmi, a cikin yarjejeniyar ƙungiyar da Gwamnatin Tarayya a cikin 2009.
Sai dai kuma ASUU ta ce kuɗaɗen da ta ke nema a riƙa kashe wa fannin ilimi, kwata-kwata ba su cikin tsarin kuɗaɗen da TETFund ke kashe wa a jami’o’i da kuma sauran manyan makarantun gaba da sakandare.
Adamu ya ce ana nan ana ƙoƙarin ganin an daidaita an kawo ƙarshen yajin aikin da malaman jami’o’i ke ci gaba da yi, wanda ya ce ya gurgunta ƙafafun fannin ilmi.
Ya ce tunanin da ake yi cewa ta hanyar yajin aiki ce kaɗai za a iya cimma biyan ɓukata, wannan kuskure ne, kuma makahon tunani ne.
Discussion about this post