Kakakin Kamfen ɗin Tawagar Takarar Bola Tinubu, kuma Ƙaramin Ministan Ƙwadago Festus Keyamo, ya bayyana cewa kusan yanzu babu sauran ‘yan ta’adda, duk gwamnatin tarayya ta murƙushe su, “sai ɗan ɓurɓushi kawai.”
Keyamo a cikin wata tattaunawa da ya yi da jaridar Daily Trust TV, ya bayyana cewa tsawon shekaru bakwai kenan ya na kare gwamnatin tarayya.
A shirin tattaunawa da aka yi da Keyamo, gayyaci Daniel Bwala, wanda shi ne Kakakin Kamfen ɗin PDP a zaɓen Shugaban Ƙasa.
Duk da irin munanan hare-haren da ake yi musamman a Arewa da waɗanda aka yi kwanan baya a yankin Abuja, duk da haka Keyamo ya ce gwamnatin APC ta rage ayyukan ta’addanci ba kamar zamanin gwamnatin PDP da ta gabata ba.
Ya ce labaran da ake watsawa na rashin ƙoƙari da kasa yin wani kataɓus, duk ‘yan adawa ne ke ɗaukar nauyin buga su a kafafen yaɗa labarai.
“Yawan nanata kasawar wannan gwamnatin ya zama tamkar wata waƙa da ‘yan adawa su ka hardace, su ke rerawa a kullum, ba tare da yin la’akari da irin gagarimin ayyukan da wannan gwamnatin ta yi ba.
“Ba su da wani abin magana sai “gwamnati ta kasa, tsaro ya ruguje.” Maganar su kenan.
“Matsalar Boko gadon ta wannan gwamnatin ta yi daga PDP. A lokacin kuwa ƙananan hukumomi 14 na Barno duk a hannun Boko Haram su ke. Wancan lokacin ƙungiyar ƙwallo ta El-Kanemi Warriors a Bauchi su ke wasannin su, saboda matsalar tsaro a Maiduguri. Amma yanzu sun koma su na wasan su a Maiduguri.
“Ban ce an kakkaɓe Boko Haram baki ɗaya ba. Amma dai idan aka duba gwamnatin da ta gabata da irin c gaban da wannan gwamnati ta samar, za a an kakkaɓe su, sai ɓurɓushi su ka rage.
Matsalar yajin aikin malaman jami’o’i ita ma Keyamo ya ce laifin Gwamantin baya ce da ta ƙulla yarjejeniyar da ta kasa cika masu tun ciki 2009. “Sai aka bar wannan gwamnatin da ‘yangwangwama.”
Discussion about this post