Manyan titunan Maiduguri sun koma jajaye a ranar Asabar, yayin da dandazon magoya bayan NNPP su ka fito ana tsuga ruwan sama, su ka tarbi ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabi’u Kwankwaso.
Kwankwaso ya ke Maiduguri ne domin ya buɗe ofishin jam’iyya na jiha kuma ya ƙaddamar da wasu ayyukan jam’iyya a can.
Maiduguri nan ne mahaifar ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na APC, Kashim Shettima, kuma ɗaya daga cikin jihohin da APC ke taƙama da yawan ƙuri’u.
Kwankwaso ya kai ziyara sa’o’i 48 da Gwamnatin Jihar Barno ta kulle sakateriyar NNPP a Maiduguri, bisa zargin an buɗe ofishin ba bisa ƙa’idar Hukumar Tsara Birane ta jihar ba. Sai dai kuma daga baya an gaggauta buɗe masa ofishin bayan ɗimbin ‘yan Najeriya sun yi Allah-wadai.
Gwamantin Barno ta ce ba tada hannu wajen rufe Ofishin, Hukumar Kula da Tsara Birane ce ta rufe shi, “kuma ta rufe shi a daidai lokacin da bai dace ta rufe ɗin ba.”
A ranar Asabar dai jirgin Kwankwaso da aka ce zai sauka Maiduguri ƙarfe 3 na yamma, ya samu jinkiri saboda ruwan sama da aka riƙa sheƙawa.
Dandazon magoya bayan Kwankwaso sanye da jajayen huluna sun fito cikin ruwan sama sun fito, duk kuwa da cewa har ambaliya ruwan ya yi a wasu wurare cikin Maiduguri.
Kwankwaso ya samu rakiyar Buba Galadima, Umar Alƙali ɗan takarar gwamnan Barno na NNPP da jagoran NNPP a Barno, Attom Magira.
Kwankwaso ya ƙaddamar da sakateriyar NNPP a Maiduguri, kuma ya yi wa jama’a jawabi.
Kwankwaso ya matuƙar nuna jin daɗin ganin yadda dandazon jama’a su ka yi dafifin fita tarbar sa, duk kuwa da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
‘Zan Yi Wa Barno Irin Aikin Da Na Yi Wa Kano -Kwankwaso:
Kwankwaso ya sha alwashin cewa idan aka zaɓe shi zai maida Maiduguri kamar yadda ya maida Kano wajen samar da ayyukan raya ƙasa, ta yadda marasa galihu da dama za su samu ayyukan yi.
“Kai, yau na ga ɗimbin jama’a kuma matasa su na tafiya a ƙasa cikin ruwa, su na yi mana jinjina, tsawon kilomita 4 zuwa inda za mu buɗe sakateriyar NNPP.
“Wannan abu ya sa min damuwa a zuciya ta, ganin cewa waɗannan dandazon jama’a fa duk masu neman canjin rayuwa ne, daga halin ƙuncin da su ka tsinci kan su.
“Da iznin Allah wannan lamari ne gwamnatin mu za ta fi maida hankali a kai, wato inganta ilmin yara da samun ayyukan yi ga matasa.
“Tambayar da ta fi faɗo min lokacin da mu ke ratsawa ta cikin wannan dandazon matasa ita ce, ta yaya za mu sake dawo masu da martabar ilmi mai inganci, wutar lantarki, tsaro da kuma inganta tattalin arzikin al’ummar Barno kamar yadda mu ka yi a Kano?
“Barno na da damar da za koma kamar Kano. Amma wasu ‘yan ƙalilan ne ke tatse dukiyar jihar. Mu kuwa idan aka ba mu dama, za mu farfaɗo da jihar, mu inganta rayuwar masu zaman dirshan a sansanonin gudun hijira ta yadda za su koma muhallin su kuma mu inganta rayuwar su domin farfaɗo masu da sana’a. Za mu samar da magunguna kyauta ga ƙananan yara, mata masu ciki da masu shayarwa.” Inji Kwankwaso.
Discussion about this post