Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da cewa Bello Turji ya amince da sulhuntawa da gwamnati. Mataimakin Gwamnan Zamfara Hassan Nasiha ne ya tabbatar da hakan a Gusau, babban birnin jihar a ranar Lahadi.
Ya ce tubar da Bello Turji ya yi ta kawo zaman lafiya a Birnin Magaji, Shinkafi da Karamar Hukumar Zurmi.
Mataimakin Gwamna ya yi wannan jawabi a wurin taron da Ƙungiyar Ɗaliban Jami’ar Madina ‘yan Jihar Zamfara su ka shirya ranar Lahadi.
Hassan ya ce ya gana da ‘yan bindigar da ke cikin ƙananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara.
“Tsawon watanni uku da su ka gabata zuwa yau, ‘yan bindiga ba su kai hari a Magami da kewayen gundumar ba. Hakan kuwa ya tabbata ne saboda sulhun zaman lafiyar da aka samu da ‘yan bindiga.” Inji Nasiha.
“Kowa dai ya san ƙasurgumin ɗan bindigar nan Bello Turji, wanda ya addabi yankin.
“Gwamnatin Zamfara ta bi ta hanyar kwamitin samar da zaman lafiya, ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da sulhu da shugaban ‘yan bindiga. Kuma ya amince ya daina wannan ɓarna da ya ke yi, ya rungumi zaman lafiya.
“Yanzu Turji ya na kashe ‘yan bindigar da ba su tuba ba, waɗanda ke addabar yankin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji.” Haka dai Mataimakin Gwamnan Zamfara ya tabbatar.
Ya ce kwamitin sulhu da zaman lafiya ya gana da shugabannin gungu-gungun ‘yan bindiga tara a sansanonin su da ke Magami da masarautar Ɗansadau. Kuma duk sun bayyana damuwar su.
“Sun ce Hausawa na kai masu hari, su na yi wa matan su fyaɗe, su na kashe Fulani idan sun je kasuwanni, kan hanyar komawar su gida.
Nasiha ya ce Gwamantin Zamfara ta bada umarnin a maida wa Fulanin dukkan burtalolin da aka ƙwace masu, dazuka, gonaki da mashayar ruwa da dabbobi da sauran kayan da Hausawa su ka ƙwace masu.
Ya ce tilas kowane ɓangare ya amince da sharuɗɗan da yarjejeniyar ta ƙunsa, domin a samu zaman lafiya mai ɗorewa a yankunan.
Fulanin sun ce gwamnati ta sakar masu matasan su da ke tsare a gidajen kurkuku da ofisoshin ‘yan sanda.
“Sun kuma buƙaci a gina masu makarantun zamani domin su kai ‘ya’yan su makaranta. Sannan kuma a gina masu ababen more rayuwa, a samar masu takin zamani da kayan noma.
“Sun ce rashin ilmi ne ke sa Bafulatani ɗan shekara 12 zai iya ɗaukar bindiga ya harbe mutum mai shekaru 70.” Inji Mataimakin Gwamna.
Shugaban Ƙungiyar Ɗalibai Kabiru Maru, ya ce sun shirya taron ne su bada na su goyon baya da gudummawar wanzar da zaman lafiya a jihar Zamfara, wadda ke fama da wannan tashin hankali tsawon shekaru goma.
Discussion about this post