Ma’aikatar (NiDCOM) ta gargadi iyaye da su daina tura ƴaƴan su yankin Arewacin Kasar Cyprus saboda tsananin rashin tsaro a wannan yankin.
Shugaban ma’aikatar Abike Dabiri-Erewa ta sanar da haka a taron da ma’aikatar ta yi da manema labarai a cikin makon jiya.
Abike ta ce an kashe dalibai ‘yan Najeriya a Arewacin kasar Cyprus da dama saboda wannan yankin har yanzu ba kasa bace mai zaman kanta, ta na karkashin ikon kasar Turkiyya ne.
Wannan kira da muka yi ya zama dole domin iyaye su san irin halin da ƴaƴan su kan shiga a wannan kasa. Babban abinda ya ci mana tuwo a kwarya shine ko da wani abu ya samu wani ɗan Najeriya babu inda zaka kai kukan ka, saboda kasar bata nan ne bata can, majalisar ɗinkin duniya bata san da ita ba.
Ko mai ya samu ɗan Najeriya sai dai mu zuba ido domin ba mu da inda zamu kai kukan mu. Dalilin haka ya sa gwamnati take kira ga iyaye ceqa abinda ya fi dacewa shine kawai a daina tura yara kasar karatu.
Ƴan Najeriya da dama na karatu a yankin Kasar Cyprus ta Arewa. Babban dalili kuwa shine ganin yadda karatu a can ke da sauke fiye da wasu kasashen.
Discussion about this post