Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, kuma ɗan APC a yanzu, Femi Fani-Kayode, ya bayyana ra’ayin da ke zuciyar sa dangane da yadda magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi ke ƙara yaɗo, kamar ɗan duma.
Cikin wani ra’ayin sa da aka buga a PREMIUM TIMES, Fani-Kayode ya ce duk da shi ba ɗan LP ba ne, kuma ba zai taɓa goyon bayan Peter Obi ba, duk da haka ya hango cewa magoya bayan sa da ake kira ‘Obidients’, za su canja alƙiblar siyasa da mulki a Najeriya nan gaba.
Fani-Kayode ya ce duk da ba ya ra’ayin tafiyar ‘Obidients’, duk da haka ba zai ƙi jinjina masu ba, ganin yadda su ka zama wata aƙida wanda tuni ta ginu a zukatan ɓangarori daban-daban na ɗimbin manya da matasa masu hanƙoron neman samun iskar sauyi daga waɗanda su ka kankame akalar mulki a ƙasar nan, wato APC da PDP.
Ya ce ko an ƙi, ko an so magoya bayan ‘Obidients’ sun zama babbar barazana ga manyan jam”iyyun ƙasar nan. Kuma ya ce wanda bai yi masu kallon barazana, to shi ta shafa.
Kayode ya ci gaba da cewa sun zama wata guguwa da ta darkako siyasar ƙasar nan mai cike da ƙurar neman kawo sauyin amshe ragamar siyasa da mulki daga hannun tsoffin ‘yan alewar da suka kafa dimokraɗiyya daga 1960 zuwa yau.
Ya ce idan aka lura, ‘Obidients’ ba su yi wa kan su kallon ‘yan siyasa, sun fi kallon kan su a matsayin masu hanƙoron kawo saurin tsarin dimokraɗiyya daga tsoffin hannu zuwa sabbin hannaye.
“Obidients’ sun rikiɗe zuwa masu aƙidar kawo sauyi, waɗanda ba masu bin ɗan siyasa su ke kallon kallon kan su ba.
Ita jam’iyya ai za ta iya mutuwa kuma ko gamin-gambiza jam’iyyu su ka yi, majar za ta iya rushewa. Amma ita aƙida idan aka ɗarsasa maka iya a zuciya, to ta zauna kenan, kankare ta abu ne mai wahala.
“Ina ganin yadda su ke nuna kishin ‘Obidients’ a coci, a makarantu, a kasuwa, a cikin gari, a kan titina, kai har a cikin ma’aikatan gida na duk ina gani.
Kayode ya ce shi dai ba ya ra’ayin su, amma fa ya na jinjina masu, saboda ya ga irin yadda su ke nuna da gaske sun gaji da irin tafiyar da ake a kai, su na neman canji.
“Ka san kuma masu karin magana na cewa mai nema ya na tare da samu, ko ba-jima ko ba-daɗe.”
Kayode ya ce ya na ganin yadda a sassan ƙasar nan daban-daban, kuma daga mabiya addinai daban-daban da ƙabilu daban-daban.
Discussion about this post