Gwamnatin Jigawa ta bada sanarwar a rufe duk makarantun Boko dake fadin jihar bisa fargabar harin ‘yan bindiga.
Sai dai kuma wannan sanarwa ya zo ne a daidai dalibai sun fara rubuta jarabawar kashen zangon karatu na wannan shekara.
Wannan hukunci da gwamnati ta yanke ba tare da dalili ba ya firgita mutane da daliban wanda suka fara tattara kayansu domin komawa ga iyayen su.
Kakakin ma’aikatar ilimi Wasilu Umar ya tabbatar da haka wa PREMIUMTIMES sai dai bai yi karin bayani a kai ba.
Shugaban daya daga cikin makarantun firamare dake garin Dutse ya bayyana cewa umarni ne aka basu na su rufe makarantu.
“An ce mu rufe makarantu har sai illa masha Allah amma muna kyautata zaton an rufe makarantun ne saboda tabarbarewar tsaro a jihar
Dalibin jeka ka dawo na makarantar gwamnati Nuhu Sanusi ya ce haka kawai aka ce musu su tafi gida ba tare da sun rubuta jarabawar su na darasin ‘ Civic Education’ da suke shirin rubutawa.
Discussion about this post