Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamiɗo, ya ragargaji Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas a kan rigingimun da ke faruwa a cikin jam’iyyar.
A wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV ya yi da shi a ranar Talata, Lamiɗo ya ce nan da watanni takwas Wike zai zama mujiyar da kowa zai riƙa gudun sa bayan ya sauka daga muƙamin gwamna da ya ke tutiya da shi a yanzu.
Lamiɗo wanda makusancin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ne, ya ce shisshigi da wuce makaɗi da rawar da Wike ke yi, ba zai haifa masa ɗa mai ido bayan ya sauka daga mulki ba.
“Shi Wike ya na halayya ce irin ta mulkin Fir’aunanci, wadda sai idan ‘yan jihar sa sun maida kan su bayi ne kaɗai za su iya bin sa.”
Lamiɗo ya yi tir da irin kakkausan kalaman da ya ce Wike na fesawa idan ya na magana tamkar wani ɗan jagaliya.
Bayanan Lamiɗo sun zo daidai lokacin da ake ta ƙoƙarin ganin an sasanta Wike da Atiku, kuma kwana ɗaya bayan an ce Wike da makusantan sa sun gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu.
“Surutai da bobbatan da Wike ke yi, ana fa tsayawa a saurare shi ne don kawai ya na gwamna. Amma ba don wani wai shi Wike ne ke magana ba.
“Ka dubi abin da ya ke yi a jihar sa. Mutum 13 ya fito takarar fidda gwani na zaɓen gwamna. Amma Wike ya yi masu ƙarfa-ƙarfa, ya ɗora wanda ya ke so. Kuma dukkan sauran sun fusata da shi.
Da ya ke magana kan masu cewa a sauke Shugaban PDP, Iyorchia Ayu saboda ya fito daga Arewa, yankin da ɗan takarar shugaban ƙasa ya ke, sai Lamiɗo ya ce shi ba ya goyon bayan a sauke shi. “Saboda ai ba wannan ne karon farko da ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito yanki ɗaya da shugaban PDP na ƙasa ba.” Inji Lamiɗo.
“A zaɓen 2007 da marigayi ‘Yar’Adua ya yi takara, Ahmadu Ali ne shugaban PDP, daga Jihar Kogi. Saboda haka ai shugaban jam’iyya ba shugaban ƙasa ba ne. Ko kaɗan ba haɗa su. Sai mu ka ce a bari sai bayan an ci zaɓe sai a sauya.” Inji Lamiɗo.
Daga cikin rigimar da ake yi da Wike dai har da neman a cire Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayu, saboda ya fito daga Arewa, yanki ɗaya da Atiku da ke takarar shugaban ƙasa.
Discussion about this post