Tawagar Kamfen ɗin TInubu (TCO) ta ja kunnen magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa a jam”iyyar LP, Peter Obi cewa su daina yaɗa labaran ɓatanci, yarfe da labaran bogin shirga wa ‘yan Najeriya ƙarairayi.
Daraktan Yaɗa Labarai na tawagar kamfen ɗin TInubu mai suna Bayo Onanuga ne ya yi wannan kira a cikin wata sanarwar da ya fitar a Abuja, a ranar Laraba.
Ya ce waɗannan ƙarairayi da yarfe ba su iya sa ɗan takara ya yi nasara a zaɓe.
Onanuga ya ja hankalin Obi cewa ya ja kunnen magoya bayan sa su kyale jama’a su riƙa tattauna batutuwa masu muhimmanci dangane da zaɓen 2023, waɗanda za su kawo ci gaba da bunƙasa ƙasa.
Ya yi wa Obi nasihar ya ja kunnen magoya bayan sa su daina yaɗa ƙarairayi, yarfe, sharri da tozarta ɗan takarar APC Bola Tinubu.
Ya ce zai fi alheri ga Najeriya idan aka daina irin shirmen da magoya bayan Obi ke yi, aka koma ana tattauna batutuwa waɗanda za su amfani ƙasar nan a zaɓen 2023, kuma za su iya fitar da ‘yan Najeriya daga ƙuncin talaucin da su ke fama da shi.
Onanuga ya ce yin wannan jan hankali ya biyo bayan wata farfagandar ƙarya da a aka watsa, inda aka ce wai Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo ya rubuta wa Tinubu wasiƙa, inda ya ba shi shawara cewa ya janye daga takara, ya goyi bayan Peter Obi, kuma ya je ya kula da lafiyar sa.
Tawagar Kamfen ɗin TInubu ta ce bayan Shugaban Ghana ya ƙaryata wannan magana, ya ce bai taɓa yin ta ba, sun gano cewa magoya bayan Obi ne su ka fara yaɗa wannan sharri.
Sannan kuma sun ce magoya bayan Obi sun wa Tinubu sharri wai ya nemi tsohon gwamnan Legas, Akinkumi Ambode ya riƙa ba shi naira biliyan 50 daga aljihun jihar a duk wata.
Tawagar Tinubu ta ce har Ambode ya sauka Legas ba ta taɓa tara naira bilyan 50 duk wata ba, ballantana har a riƙa yin kyauta da su.
Discussion about this post