Kai tsaye ba tare wata shimfiɗa ko gabatarwa ba, ya kamata mai karatu ya fahimci cewa tsohon Gwamnan Jihar Anambra Willie Obiano da ya sauka watannin baya ranar da aka rantsar da sabon Gwamna Charles Soludo a Jihar Anambra, shi ne gwamna na 31 da EFCC ta taɓa kamawa ta garƙame bayan saukar sa daga mulki.
Ana zargin Obiano ya yi matashin kai da buhun kuɗi ɗauke da naira biliyan 42.
Daga cikin waɗannan 31, bakwai kaɗai kotu ta taɓa samu la laifi, ta yanke masu hukunci. Haka kuma kotu ta sallami ɗaya daga cikin su, ta ce bai taɓa wawurar ko ƙarfamfana ba.
Daga cikin waɗanda aka kama da laifin ɗibga shirgegiyar sata, akwai gwamnoni biyu da ke tsare a kurkuku, waɗanda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi masu afuwa kwanan nan, aka sake su, saboda dalilai na tsufa da rashin lafiya.
Tsohon Gwamna Rochas Imo Rochas Okorocha ne na baya-bayan nan da EFCC ta damƙe. Amma dai shi ma ta sake shi a ranar da ya je gaban kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, a Abuja, kafin zaɓen fidda gwani.
Daga Janairu zuwa Satumba, 2021, EFCC ta gurfanar da mutum 978 da aka yanke masu hukunci. Sai dai kuma daga cikin su, mutum biyu ne fitattu a cikin su, wato Abdulrashid Maida da Faruq Lawan.
1. Abdul’aziz Yari: Mai Tsoron Aradu Shi Ta Ke Faɗawa:
Shi ne tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, kuma tsohon shugaban ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF). EFCC ta sha tsare shi ana yi masa tambayoyin ‘yar-ƙure, amma a babbar tuhumar da ake masa, ba a taɓa gurfanar da shi a kotu ba.
Cikin 2021 EFCC a Legas ta tsare shi dangane da wani yunƙuri da ya yi ya nemi karkatar da naira biliyan 300 daga wani asusun banki zuwa wani bankin daban. Lamarin ya faru a cikin Fabrairu, 2021.
Cikin Afrilu kuma Yari ya bayyana a ofishin EFCC da ke Sokoto.
Kuma baya-bayan nan wannan jarida ta buga labarin yadda Yari ya taya tsohon Akanta Janar Ahmed Idris jida, lodi da jigilar naira biliyan 84.
EFCC har ma ta bayyana yadda Yari ya yi bindiga da dala 700,000 wajen ɓalle bushasha da sayen kayan alatu a Saudiyya, lokacin Umrah ta 2022.
2. Theodore Orji na Abiya: Turutuwa Uwar Jida:
Bayan saurar sa daga Gwamnan Jihar Abiya, ba a kama shi ba sai bayan da ya zama sanata. An damƙe shi cikin Agusta, 2022 a filin jirgin saman Abuja, tare da ɗan sa. Sai dai kuma bayan kwanaki an sake shi, aka ce ya riƙa zuwa ofishin EFCC ɗin ana yi masa tambayoyi.
An zarge shi da yin bindiga da naira miliyan 500 duk wata ta kuɗaɗen tallafin tsaron jiha, na tsawon shekaru takwas, daga 2007 zuwa 2015.
An ce ya zaizaye wata naira bilyan 2 ta kuɗin aikin magance zaizayar ƙasa da wasu kuɗaɗen Sure-P.
Masu ƙorafi daga Save Nigeria Group sun zarge shi da karkatar da Naira biliyan 383 daga Asusun Gwamnatin Tarayya. Sai wata naira bilyan 55 ta kason rarar ribar ɗanyen mai, naira bilyan 2.3 na Sure-P.
Sannan akwai wasu naira bilyan 10.5 na bashin da ya ciwo wa jihar, amma ya haɗiye, Naira biliyan 12 na Paris Club da Naira biliyan 55 na ASOPADEC.
An zargi ɗan sa Chinedu da mallakar asusun ajiyar kuɗaɗen sama da 100 a bankuna daban-daban.
3. Tanko Almakura: Kurege Mai Ƙofa 55:
Ya yi Gwamnan Nassarawa daga 2011 zuwa 2015. Cikin 2021 EFCC ta kama shi bayan ya shiga majalisar dattawa, cikin 2021. An damƙe shi tare da matar sa, bisa zargin sun riƙa karkatar da kuɗaɗe a wasu asusun ajiya a bankuna, mallakar sa da matar sa da kamfanonin sa, har asusu 55.
Akwai asusun da aka ajiye dala 250 kaɗai a cikin sa bayan ya zama gwamna. Amma daga nan sai asusun ya riƙa cika maƙil da ƙazaman kuɗaɗe, kamar mai tu’ammali da rauhanai.
4. Godswill Akpabio: ‘Marar Gaskiya Ko Cikin Ruwa Zai Yi Gumi’:
Tun bayan saukar sa a 2015 aka fara zargin cewa ya ɗirka sata. Har wata rana ya yi hatsarin mota a Abuja, lokacin da yake hanzarin zuwa filin jirgin sama ya hau jirgi zuwa Akwa Ibom, bayan ya samu labarin jami’an tsaro sun fasa wani ɗakin sa an ga maƙudan kuɗaɗen, malala-gashin-tinkiya.
An zarge shi da yi wa sama da naira biliyan 100 haɗiyar kafso. Ya ce dai ƙarya ake yi masa. Da ya haɗiyi kuɗaɗen da an ga cikin sa ya koma kamar tulu.
Jaridar Shahara Reporters ta taɓa buga labarin cewa Akpabio ya yi ƙoƙarin bai wa Abdulrashid Bawa toshiyar bakin dala 350,000, amma dai. Amma dai tsohon Ministan na Hukumar Neja Delta ya ce ƙarya ake yi masa.
5. Abdulfatah Ahmed Na Jihar Kwara: Kaɗan Mai Ban Haushi:
Ya yi Gwamnan Kwara daga 2011 zuwa 2019. An kama shi cikin watan Mayu, bayan an zarge shi da karkatar da naira bilyan 9. Ya yi kwana biyu a hannun EFCC, daga nan tun da aka sake shi, har yau ba a gurfanar da shi kotu ba shi ma.
7. Aliyu Wamakko, Sokoto:
EFCC ta zarge shi da laifin karkatar da naira biliyan 15 lokacin ya na Gwamnan Jihar Sokoto. Amma dai har yau ba a gurfanar da shi kotu ba.
8. Ali Modu Sheriff, Barno: Kamar Maza Ta Na Ga Muzuru:
Ya yi Gwamna a daga 2003 zuwa 2011. An yi zargin ya karkatar da Naira biliyan 300. Tun cikin 2018 EFCC a Abuja ta gayyace shi, inda aka zarge shi da karkatar da dala miliyan 200 wajen ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta da Boko Haram a cikin wata maƙauciyar ƙasa kusa da Barno, a cikin 2014, kamar yadda jaridar Vanguard ta buga.
Shi ma dai har yau ba a kai shi kotu ko sau ɗaya ba.
8. Rabi’u Kwankwaso:
An zargi Kwankwaso da karkatar da naira bilyan 10 tsakanin 2011 zuwa 2015. Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa mai yiwuwa EFCC ta sake kakkaɓe fayil ɗin binciken a cikin 2022 ɗin nan a lokacin da ya fito takarar shugabancin ƙasa.
9. Willie Obiano, Anambra: Tsuntsu Mai Wayo, A Tasha Ake Kama Shi:
Watannin baya ya sauka daga mulki, inda EFCC a Legas ta kama shi a filin jirgi, lokacin da ya ke ƙoƙarin arcewa zuwa Amurka. Ana neman naira biliyan 42 a hannun sa.
10. Bukola Saraki: ‘Buzun Kura Firgita Karnai’:
Tun bayan saukar Saraki daga mulkin jihar Kwara ake ta karankatakaliya da shi, amma har yau ba a maka shi kotu ba. Ya sha cewa bi-ta-ƙulli ne kawai ake yi masa.
11. Bola Tinubu: ‘Mai Kaza Aljihu Ba Ya Jimirin As’:
Cikin shekarar da ta gabata ne Shugaban EFCC AbdulRashid Bawa ya ce EFCC na binciken Tinubu kan ƙaryar da ya ce ya kantara wajen rantsuwar mallakar kadarori.
An daɗe ana zargin Tinubu dangane da yadda ta tara maƙudan kuɗaɗe bayan ya zama Gwamnan Jihar Legas data 1999 zuwa 2007.
Ministan Shari’a Abubakar Malami ya ƙaryata cewa wai ana binciken Tinubu. Ya ce ba a binciken sa. Amma kwafen wata takarda da jaridar Peoples Gazette ta buga, takardar mai ɗauke da ranar 6 Ga Nuwamba, 2020, ta nuna cewa EFCC na binciken sa.
Kuma takardar da ɗauke da sa hannun Bawa, wanda a yanzu shi ne Shugaban EFCC.
Discussion about this post