Wata mata da ake zargi ƴar maɗigo ce ta kashe mijin abokiyar ta da wuka a kauyen Onitsha dake karamar hukumar Ontisha ta Kudu a jihar Anambra.
Wannan mummunar abu ya auku ranar Talatar makon jiya da misalin karfe 9:20 na dare.
Magidancin da aka kashe mai suna Ikechukwu Onuma ma’aikacin kwalejin kiwon lafiya ne dake Onitsha sannan ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya dawo gida ya iske matarsa da ƙawarta kwance kan gado suna aikata maɗigo.
Matar mamacin Nkemdili ta tsere a lokacin da ta ga mijinta ya yanke jiki ya faɗi kasa muce bayan ƙawarta ta daɓa masa wuka.
Mutane sun ce marigayi Onuma bai san cewa matarsa Nkemdili ta dade tana buga irin wannan harka da mata ba.
Kakakin rundunar Tochukwu Ikenga ya tabbatar da kisan sannan ya ce rundunar ta kama Ebele Onochie yanzu tana tsare a ofishinsu.
Ikenga ya ce kwamishinan ‘yan sanda ya bada umurnin Kai karan zuwa ga fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin hakq domin gudanar da bincike.
“Onuma ya rasu a lokacin da likita ke duba shi a asibiti.
Zuwa yanzu ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike akai.
Dokar hana liwadi da madigo a Najeriya.
A shekarar 2014 ne gwamnatin Najeriya ta saka dokar haramta luɗu da madigo a kasar nan.
Bisa ga dokan hukuncin duk wanda aka kama yana
ko rana aikata haka za a ɗaure shi na tsawon shekara 14.
Discussion about this post