Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da kitimirmirar da Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed da Ministan Shari’a Abubakar Malami su ka ƙulla domin ya amince a fara ɗibar kuɗaɗen jihohi ana biyan wasu ‘yan gidogar kwangila, alhali rikicin biyan kuɗin na kotu ba a kai ga yanke hukunci ba.
PREMIUM TIMES ta ji cewa a wurin taron Majalisar Zartaswa na ranar 3 Ga Agusta ne Buhari ya bayar da umarnin kada a fara cirar kuɗin, bayan ya rigaya ya sa hannun amincewa a baya.
PREMIUM TIMES ta buga labari cikin makon da ya gabata, dangane da yadda Gwamnonin Najeriya su ka rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari wasiƙar rashin amincewar su a fara cirar kuɗaɗen.
Daga baya PREMIUM TIMES ta gano cewa yayin da gwamnonin su ka ga Minista Zainab da Malami sun matsa ƙaimin a fara cire kuɗaɗen a yanzu, alhali kuma ana cikin tafka shari’a a kotu, kuma Ƙarin Ƙoli ta bada umarnin kada a fara cirar kuɗaɗen sai an kammala shari’a tukunna tsakanin ‘yan gidogar dillancin kwangilar da ake rigima da su tukunna.
Yayin da Ministoci su ka hallara wurin taron Majalisar Zartaswa, sai Minista Zainab da Malami su ka bijiro batun cewa Shugaba Buhari ya gaggauta amincewa a fara biyan kuɗaɗen kawai.
Ministocin Sun Ƙi Amince Wa Minista Zainab da Malami:
Kafin a kai ga zuwa taron Majalisar Zartaswa, tuni gwamnonin Najeriya sun rubuta wa ministoci wasiƙu a asirce cewa su na roƙon idan sun je taron, kada su goyi bayan buƙatar Zainab Ahmed da Abubakar Malami, idan su ka nemi Buhari ya da hannun amincewa a fara cirar kuɗaɗen.
An shiga taron bayan Zainab da Malami sun gabatar da Buƙatar su ga Buhari, an da nan sai Ministoci su ka bijire wa Malami da Zainab. Wanda ya fara magana shi ne Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola.
Fashola ya ce karya doka ce ƙarara idan aka fara kamfatar kuɗaɗen gwamnoni ana biyan bashin da ba shi da tabbas, saboda shari’ar na kotu. Kuma Kotun Ƙoli ta bada umarnin dakatar da biyan kuɗaɗen.
Haka kuma Fashola ya ce bai kamata a fara biyan kuɗaɗen ba, a wannan hali mawuyaci da Najeriya ke ciki, yadda ta kai har biyan albashi ma neman zama jidali. Sannan kuma ga ƙarancin kuɗaɗe a asusun gwamnatin tarayya.
Shi ma Ƙaramin Ministan Ƙwadago Festus Keyamo da sauran wasu ministoci duk su ka ƙi amincewa a fara cirar kuɗin, har sai an ga ɓangaren da kotu ta bai wa gaskiya tukunna.
Daga nan Buhari ya umarci Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed cewa kada ta sake ta fara sakar wa waɗanda ke rigima da gwamnonin kuɗaɗe tukunna, sai an kammala shari’ar da su ke da gwamnoni, an san sun cancanta ko ba su cancanta ba tukunna.
Bibiyar Labaran Rikicin Kamashon Kuɗaɗen Paris Club:
Cikin makon jiya ne PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa yunƙurin fara cirar dala miliyan 418 daga aljihun jihohi 36 ya haɗa Gwamnoni da Gwamnatin Tarayya gagarimar rigima.
Gwamnonin Najeriya a ƙarƙashin Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), sun ƙi amincewa Gwamantin Tarayya ta fara cirar dala miliyan 418 daga asusun gwamnatocin jihohi, domin biyan wasu dillalan da ke iƙirarin sun yi gada-gadar da su ka cancanci su ci kuɗaɗen.
A cikin wata wasiƙa da NGF ta aika wa Gwamantin Tarayya ta hannun Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, gwamnonin sun ce duk wani azarɓaɓin da Gwamnatin Tarayya za ta yi don ta gaggauta fara cirar kuɗin, to haramtacce ne, domin a yanzu haka maganar ta na gaban Kotun Koli. Kuma ita Kotun Ƙoli ɗin ta hana a ciri kuɗaɗen tukunna.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya sa wa wasiƙar ƙin yarda a fara cirar kuɗin hannu.
A cikin wasiƙar, sun gargaɗi Ministan Shari’a Abubakar Malami da Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed cewa duk wani ƙulomboton da za su yi don a fara cirar kuɗin, to su sani karya dokar Kotun Ƙoli ce.
Duk wani ƙoƙarin da Minista Malami ya yi har ya sa Buhari ya da amincewa a fara cirar kuɗaɗen, ya haɗu da biirewa da ƙin amincewa daga Gwamnonin Najeriya.
Gwamnonin sun ce tilas tunda batun ya na gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara, to ba su yarda a fara cirar kuɗaɗen ba tare da jiran a ji hukuncin da kotu za ta bayyana ba.
Yunƙurin neman fara cirar kuɗaɗen ya zo ne bayan da wani daga cikin dillalan gada-gada mai suna Riok Nigeria Limited, wanda Gwamnatin Tarayya ta bai wa rubutaccen alƙawarin kuɗin kamasho dala miliyan 142 ya garzaya Kotun Ƙoli, bayan shari’a ta kayar da shi a Kotun Ɗaukaka Ƙara.
Ya maka Ƙungiyar Gwamnonin Kotun Ƙoli, inda a ranar 3 Ga Yuni Kotun Ƙoli can ma ta kori ƙarar da ya shigar.
Gwamnonin Najeriya sun ce haramun ne a fara cirar kuɗaɗen su a biya dillalan gada-gadar, tunda Kotun Ƙoli ta ce NGF ko ALGON ba su da hurumin bayar kwangilar da za a ciri kuɗi daga kuɗin su da ke aljihun gwamnatin tarayya a biya masu iƙirarin sun yi kwangilar.
“Don haka korar ƙarar RIOK NIGERIA Ltd da Kotun Ƙoli ta yi, ta shafi miliyoyin dalolin da sauran ‘yan gada-gadar su uku ke neman a biya su.
Salsalar Daɗaɗɗen Rikicin:
Yadda Kotu Ta Hana Kwasar Dala Miliyan 418 Daga Kuɗaɗen Jihohi A Biya Dillalan Gada-gada:
A ranar Juma’a ce Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta dakatar da Gwamnatin Tarayya kwasar dala miliyan 418 daga asusun jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774, da nufin ta biya wasu dillalan gada-gada masu iƙirarin cewa sun yi wa jihohi da ƙananan hukumomi ayyukan adadin kuɗaɗen a shekarun baya.
Dillalan gada-gadar sun ce sun yi wa jihohi da ƙananan hukumomi aikin tuntuɓa ne da wasu kwangiloli tsakanin 1995 da 2002, wajen ƙoƙarin aikin dawo masu da kuɗaɗen da aka riƙa ɗibar masu ana biyan bashin Paris Club da London Club.
Babban Mai Shari’a Iyan Ekwo ya umarci Gwamnatin Tarayya ta dakatar da fara kwasar kuɗaɗen da ta shirya fara kwasa daga watan Nuwamba, har sai bayan an kammala shari’ar da Gwamnonin Najeriya 36 suka shigar a gaban sa.
Gwamnonin 36 sun shigar da ƙarar ta hannun gogaggun lauyoyin su biyu, Jibrin Okutedo da Ahmed Raji, waɗanda dukkanin su manyan lauyoyi ne (SAN).
A ƙarar da su ka shigar, lauyoyin sun shaida wa kotun cewa Gwamnoni 36 na Najeriya ba su yarda cewa waɗancan dillalan gada-gadar sun yi ayyukan da su ka ce sun yi a jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774 a shekarun baya ba.
Lauyoyin sun ce masu iƙirarin sai an biya su haƙƙin kuɗaɗen har dala miliyan 418, ‘yan gidoga ne kawai, lamarin babu gaskiya a ciki.
“Kuma idan Gwamnatin Tarayya ta kwashi kuɗaɗe a asusun jihohi 36, to jihohin za su kasance a talauce, ta yadda biyan albashi ma ba zai yiwu ba.”
Daga cikin waɗanda gwamnoni 36 su ka kai ƙara, har da Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe ta Tarayya, Ma’aikatar Harkokin Shari’a da Antoni Janar, kuma Ministan Shari’a da kuma Ofishin Bin-diddigin Kuɗaɗen Bashi (DMO) da kuma Kwamitin Rabon Kuɗaɗen Kasa na Gwmnatin Tarayya, wato FAAC.
wanda Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta bayar a ƙarar da su ka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/148/2017.
Nwodo na neman a biya shi dala miliyan 142,028,941.
Sai kuma wasu mutum uku da ke neman a biya su dala miliyan 143,463,577.76 a ƙarar da su ka shigar mai lamba FHC/CV/2129/2014.
Su ukun sun haɗa da Riok Nigeria Ltd, Orji Nwafor Orizu da wani mai suna Olaitan Bello.
Wanda ya fi saura kason kuɗaɗe a cikin su shi ne Iseghoghi Edwards, mai dala miliyan 159. A bisa hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta zartas mai lamba FCT/CV/1545/2015.
Akwai kuma kamfanin wani mai suna George Uboh, wanda zai karɓi dala miliyan 47,831,920.
Discussion about this post