Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa za a bude kwalejin ilimi na Shehu Shagari ranar 8 ga Agusta 2022.
A wata sanarwa da rajistarar kwalejin Gandi Asara ya fitar ya ce za a bude kwalejin ne bayan hukuncin da hukumar makarantar ta yanke na a bude makarantar.
Gwamnan jihar Aminu Tambuwal ya umurci hukumar kwalejin da ta zauna domin tsaida ranar bude makarantar nan ba da dadewa ba.
Tambuwal ya bada wannan umurin ne bayan ya karbi rahotan da kwamitin da ya nada domin gudanar da bincike kan kisan dalibar makarantar da aka yi a kwanakin baya.
Bude kwalejin
Bisa ga sanarwar da Asara ya fitar ranar Alhamis za a bude kwalejin ranar 8 ga Agusta 2022.
Sai dai kuma kowani dalibi zai biya naira 1000 tare da gabatar da rubutaccen alkawari da rantsuwa sannan da saka hannu a takardar makarantar na zai zauna lafiya.
Idan ba a manta ba a watan Mayu gwamnatin jihar Sokoto ta rufe Kwalejin Ilimi na Shehu Shagari dake jihar Sokoto a sanadiyyar barkewar rikici adalilin daukar hukuncin da dalibai suka yi inda suka kashe wata daliba maisuna Deborah, bayan ta yi batanci ga fiyayyen halitta SAW.
Ita dai Deborah ta fusata ne wai don wasu ɗalibai sun saka abubuwan addini a cikin guruf din WhatsApp din da suke ciki.
Da yake ya zo da karewar kwana sai ta yi kaman batanci ga Annabi SAW, wanda hakan yasa matasa suka fusata suka bita suka kasheta ta hanyar Jifa da duka.
Discussion about this post